Jonathan ya yi karin haske kan batun sake takarar shugaban kasa a 2023

Jonathan ya yi karin haske kan batun sake takarar shugaban kasa a 2023

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta rahoton da aka wallafa na cewa ana tursasa shi a kan ya fito takara a 2023

- Kamar yadda mai magana da yawunsa ya sanar, ya ce tsohon shugaban kasar na ta kokarin ganin kafuwar gidauniyarsa

- An gano cewa, kafafen yada labarai masu karantar nagarta ne suka dinga wallafa wannan labarin

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta rahoton da aka wallafa a mujallu cewa wasu masu ruwa da tsaki su takura shi don fitowa takara a zaben 2023.

A takardar da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar yace tsohon shugaban kasar ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da lumana da zaman lafiya a damokaradiyyar Afirka.

Goodluck Jonathan ya nuna mamakinsa a kan labarin da ya dade yana yaduwa.

DUBA WANNAN: Trump ya yi amai ya lashe kan barazanar kai hari wuraren tarihi a Iran

Ya ce; "Babu wani abu makamancin hakan. Tsohon shugaban kasar bai yi wannan maganar ba kuma bai tattauna hakan da kowa ba kafin zuwan zaben."

"Yana kokarin gina gidauniyarsa ne mai suna Gidauniyar tallafi ta Goodluck Jonathan don tabbatar da damokaradiyya mai dorewa da karfafa matasa a Afirka. Idan ka duba yanar gizo, zaka ga cewa kafafen yada labarai masu karancin inganci ne suka wallafa wannan labarin." in ji shi.

"Lokacin farko da wannan labarin ya fara yaduwa a yanar gizo shine kafin zaben 2019. Daga nan bai sake tasowa ba. Abun farin cikin shine yadda 'yan Najeriya suka gane cewa duk labaran kanzon kurege ne. Saboda hakan ne mujallu a kasar nan wadanda suka san abinda suke yi basu wallafa ba." a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel