Sojoji sun mayar wa Gwamna Zulum martani kan zargin da yayi musu

Sojoji sun mayar wa Gwamna Zulum martani kan zargin da yayi musu

A ranar Talata ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa zargin da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, zai iya sakarwa sojojin guiwa a kan aiyukan da suke yi a babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Duk da rundunar tayi alkawarin bincike a kan zargin, ta ce wannan zargin zai iya sa yaki da ta'addanci a kasar nan yayi kasa.

A gaggauce ne gwamnan ya karba martanin cewa rundunar zata yi bincike, amma yayi shiru a kan kalubalen da tsaro zai iya fuskanta.

A wani shingen da jami'an tsaron ke aiki ne a babbar hanyar, Gwamna Zulum ya fusata tare da zargin sojin na karbar N1,000 daga hannun matafiyan da basu da katin shaidar zama dan kasa.

Amma rundunar sojin, ta bakin babban jami'in yada labaransu, Col. Aminu Iliyasu, yace "a matsayin sojojin na kwararru kuma masu tsananin tarbiya, ba zasu dauka wannan zargin da wasa ba, balle kuma da ya fito daga bakin gwamnan jihar."

DUBA WANNAN: Matasa sun yi zanga-zanga kan sakin wasu masu garkuwa da mutane a Adamawa

A wata takarda da Iliyasu ya mika ga manema labarai, "an jawo hankalin rundunar sojin Najeriya a kan wani labari dake yaduwa a kafafen yada labarai. A labarin, an bayyana yadda gwamnan ya fusata tare da tuburewa yana wa sojoji fada a kan karbar N1,000 da suke yi a kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu. Hakan na sanya matsaloli tare da wahalhalu ga matafiya."

Ya kara da cewa, "Ya kamata a gane cewa hakan zai iya rage kaimin sojojin wajen yakar ta'addanci a kasar nan. Hakazalika, zai iya rushe nasarorin da aka samu a baya wajen yakar ta'addanci a fadin kasar nan."

Rundunar sojin ta jaddada cewa zata yi bincike mai tsanani a bangarorin, kuma zata tsamo jami'an dake wannan mugun aikin.

Iliyasu yace: "A rubuce yake a tarihi cewa, a duk lokacin da aka samu irin wannan lamarin kuma ya shafi rashin da'a, rundunar sojin bata kasa a guiwa wajen zakulowa tare da hukunta wadanda abun ya shafa."

Amma kuma, Zulum ya jinjinawa matakin gaggawar da rundunar sojin ta dauka. Ya ce yana farin ciki a kan matakin da suka ce zasu dauka.

"Gwamna Zulum na matukar farin cikin matakin da hedkwatar rundunar sojin ta dauka." In ji mai magana da yawunsa, Isa Gusau, a wata takarda da ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel