Kungiyar Ma’aikatan Najeriya sun ja daga da Gwamnoni 26 kan karin albashi
Kungiyar ‘Yan kwadago na Najeriya watau NLC, ta yi magana game da batun soma biyan sabon tsarin albashi na akalla N30, 000 ga Ma’aikata.
Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba, shi ne ya yi wannan jawabi a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a makon nan.
NLC ta bayyana cewa kawo yanzu Jihohi 10 ne kawai a cikin 36 su ka karkare magana game da yadda za a fara biyan karin albashin da aka yi.
A daidai wannan lokaci kuma akwai jihohi uku – Kuros Riba, Kogi, da Taraba, da ba a soma zama da ‘Yan kwadago a game da maganar karin ba.
“Wadannan jihohi ba su ma kafa kwamitin da za su tattauna ba, kuma ba su nuna cewa da gaske za su fara dabbaka sabon tsarin albashin ba.”
KU KARANTA: Gwamnati ta fitar da lokacin biyan karin albashin Ma'aikata
“Za mu zauna da su, dole a samu lokaci a kammala wannan magana. Domin idan mu ka jira lokaci ya tafi, bashin albashin zai taru ya cabe.”
Kason karshe na Jihohin kasar su ne su ka fara biyan wannan kari kamar yadda gwamnatin tarayya ta soma. Jihohin su ne Legas da Kaduna.
Wabba ya bayyana cewa a Adamawa, Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, da kuma jihar Ebonyi, an gama duk wani zama da za ayi.
Har gobe akwai sauran Jihohi 23 da su ke tsakiyar tattaunawa domin ganin yadda za a shawo kan karin albashin da gwamnati ta yi a bara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng