Radadin canji: Magidanci ya sauya sunan yaronsa daga Buhari zuwa Kwankwaso a Gombe

Radadin canji: Magidanci ya sauya sunan yaronsa daga Buhari zuwa Kwankwaso a Gombe

A wani lamari da ya zo cike da bada mamaki kuma tamkar almara, wani mutum mai shekaru 45 kuma magidanci, uban yara masu yawa mai suna Salisu Matagwa, na kwatas din Kumbiya-kumbiya dake Gombe, ya tara dangi da abokan arziki don taron canjin sunan daya daga cikin 'ya'yansa tara. Ya rada wa yaron suna Buhari amma ya mayar masa da Rabiu Kwankwaso.

Don yin suna gamsasshe kamar yadda addini ya tanada, ya yanka katon ragonsa tare da hada walima ga 'yan uwa, abokan arziki da mawakbta. Ya ce hakan ya zama dole ne saboda ya tsare dan sa daga tozarta, wulakanta tare da harin jama'a wadanda ke tunanin Shugaba Buhari yayi wa takwara.

A yayin da ya zanta da jaridar Tribune Online a Gombe ta waya, Salisu Matagwa ya ce ya rada wa yaron sunan Buhari da farko don karrama wani kakakin majalisa mai suna Salisu Buhari. Amma ya koka da yadda jama'a ke ganin kamar Muhammadu Buhari ya yi wa takwara. Ya ce wannan cigaban bai yi msihi dadi ba ko kadan.

DUBA WANNAN: Darektan hukumar kwana - kwana ta Kano ya mutu

Ya bayyana rashin gamsuwarsa da yanayin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa da a kowacce rana yana cire rai ne a fannoni da dama, saboda abinda ya kwatanta da rashin iya salon mulki da dokokin da basu dace ba. Hakan kuwa na kawo wa talakawa matsaloli da dama.

Hakan kuwa yasa ake kalubalantar gwamnatin kuma wasu a waje ke tsangwamar dan sa da sunan Buhari

Salisu Magwata wanda ya bayyana bacin ransa karara, yace wannan abun yayi shi ne don tseratar da dan sa daga hare-haren da zasu iya cigaba da isowa ko nan gaba daga fusatattun 'yan kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel