An sako gwamnan APC a gaba a kan kokarin korar musulmai daga jiharsa

An sako gwamnan APC a gaba a kan kokarin korar musulmai daga jiharsa

Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta caccaki gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Odunayo Akeredalu a kan zarginsa da ake da kokarin korar musulmai daga jihar.

Wata zanga-zangar lumana da musulman suka yi ta tashi, bayan da jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa su a jiya Litinin, 6 ga watan Janairu, 2020.

An gano cewa, an fitar wa da Ansar-Ud-Deen kayansu daga makarantar firamare da ke Oke-Agbe Akoko a jihar Ondo ta karfin tsiya.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da MURIC ta fitar tare da mika ta ga manema labarai a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, 2020.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya kwatanta wannan aikin da gwamnatin jihar Ondo tayi da rashin dacewa, da kuma yunkurin fusatawa. MURIC ta kwatanta wannan abu da yunkurin fatattakar musulmai daga jihar. Wannan sauya halayyar kasar Yarbawa ce da aka santa da jurewa addinai da al’adu daban-daban.

DUBA WANNAN: Kissan Soleimani: NSCIA ta gargadi matasan Najeriya kan yin zanga-zanga

Kamar yadda takardar tace, “MURIC ta samu wasika daga musulman yankin Oke-Agbe Akoko a jiya. Jami’an tsaro dauke da makamai suka fitarwa da Ansar-Ud-Deen kayansu daga makarantar firamare ta karfi da yaji. Wannan lamarin kuwa bai yi mana dadi ba.”

Wasikar ta ce, ”Kamar yadda wasika mai kwanan wata 16 ga watan Disamba 2019 wacce makarantar ta samu daga gwamnatin jihar, ta umarci shugaban makarantar da ya mika ta hannun hukumar jami’ar Adekunle Ajasin. A don haka ake bukatar Ansar-Ud-Deen da su kwashe kayansu. Rashin kwashewar ne kuwa ya jawo kwashe musu da ‘yan sanda suka yi.”

“Wannan wasikar kuwa tana bayyana kyamar musulunci ne da rashin son zaman lafiya. Akwai wasu makarantun addinin Kirista dake jihar, amma ba a taba su ba. Me zai sa ba a taba wadancan ba?” in ji wasikar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164