Yaki da ta’addanci: Babatun da kake yi zai iya mayar da hannun agogo baya – Hukumar Soji ga Gwamna Zulum

Yaki da ta’addanci: Babatun da kake yi zai iya mayar da hannun agogo baya – Hukumar Soji ga Gwamna Zulum

Rundunar Sojin kasa ta Najeriya ta bayyana fadan da gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum aka dauke shi yana yi ma Sojoji a matsayin abin da ka iya kashe ma Sojoji kwarin gwiwa, kuma ya mayar da hannun agogo baya ga nasarar da aka samu da Boko Haram.

A cikin wani bidiyo dake yawo a shafukan sadarwa, an hangi gwamnan yana yi ma Sojoji tsawa tare da zarginsu da karbar cin hancin N1000 daga hannun direbobin dake bin babbar hanyar Maiduguri – Dammaturu.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar Kaduna

Cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaru na Operatiob Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa babatun da gwamnan yake yi zai yi kawo tasgaro ga nasarorin da dakarun rundunar suka samu a yaki da ta’addanci.

“Yana da kyau mu bayyana cewa irin wannan babatu daga bakunan manyan mutane musamman kamar gwamnan jaha zai iya mayar da hannun agogo baya a yaki da ta’addanci da sauran miyagu a duk fadin kasar nan.

“Mun ga wannan bidiyo, kuma zamu yi bincike a zargin karbar cin hanci da gwamnan ya yi ma Sojoji domin rundunar Sojan kasa ba ta wasa da zargin cin hanci da rashawa saboda runduna ce mai ladabi, tarbiyya da kuma tsari.

“Kuma a inda muka kama wani jami’in Soja da laifi, zamu dauki matakin ladabtarwa a kansa kamar yadda dokokinmu suka tanadar a Act CAP A20 na dokokin Najeriya.” Inji shi.

Daga karshe Aminu ya jaddada manufar rundunar Sojan kasa ta Najeriya na cigaba da aikin da ta saba yi na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, da sauran miyagun ayyuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel