An harbe mutum daya yayin da dakatattun shugabannin kananan hukumomi suka so komawa aikinsu ta karfin tsiya
Tsananin tashin hankali ya auku tsakanin dakatatun shuwagabannin kananan hukumomin jihar Imo da kwamitin rikon kwarya na jihar. A jiya babban rudani wanda yayi ajalin mutuwar wani kansila ya auku. Hakan ya biyo bayan da wani dan daba ya harbi kansila a yayin da yake kokarin shiga ofishinsa bayan an dakatar dashi.
Dakataccen kansilan wanda aka gano sunansa da Ahamuele Maduabuchi ya mutu ne bayan da aka harbesa a Umunugba, babbar hedkwatar karamar hukumar Isu ta jihar Imo a yayin da yake kokarin shiga ofishinsa.
Haragitsin ya tashi ne a ranar Litinin bayan da dakatattun shugabannin kananan hukumomin da kansilolinsu suka mamaye hedkwatar kananan hukumomin 27 na jihar.
Sun yi biyayya ga hukuncin kotun koli wanda ta yanke tsakanin shugabannin kananan hukumomin jihar Ekiti da gwamnatin jihar. Kotun tace gwamnan jihar bashi da hurumin dakatar da shugabannin kananan hukumomin.
DUBA WANNAN: Kissan Soleimani: NSCIA ta gargadi matasan Najeriya kan yin zanga-zanga
Amma kuma sai suka ci karo da jajirtattun shuwagabannin rikon kwarya wanda hakan ya kawo tashin-tashina. Shuwagabannin kananan hukumomin wadanda aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun ce sunyi komai ne karkashin hukuncin kotun koli.
Dakatattun shuwagabannin kananan hukumomin sun gayyato mabiyansu inda shugabannin rikon kwaryar suka kwaso magoya bayansu, inda aka yi gumurzu.
Mai bada shawara na musamman ga tsohon gwamna Rochas Okorocha, Sam Onwuemeodo yace shuwagabannin kananan hukumomin sun koma aiki ne saboda biyayya ga hukunci tare da dokar kotun koli.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olaniyi Fafowora, ya bada umarnin bincike a kan lamarin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng