Shekau ya mayar wa da gwamna Zulum martani, ya zarge shi da rashin sanin Al-Qur'ani

Shekau ya mayar wa da gwamna Zulum martani, ya zarge shi da rashin sanin Al-Qur'ani

Rahotanni sun bayyyana cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi watsi da kiran gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum, a kan bukatar su rungumi sulhu domin a samu zaman lafiya.

Sai dai, yayin da gwamna Zulum ke kira ga mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram a kan bukatar su ajiye makamansu a yi sulhu don a samu zaman lafiya, Shekau ya ce yaki ma yanzu suka fara, a saboda haka babu maganar sulhu.

Wani dan jarida ne mai kusanci da kungiyar Boko Haram, Ahmad Salkida, ya fara wallafa martanin na Shekau a ranar Lahadi a cikin wasu gajerun sakonni da ya fitar a shafinsa na Tuwita.

A cewar Salkida, Shekau ya yi watsi da tayin da Zulum ya yi musu duk da yin hakan tamkar wani gata ne da maslaha da gwamnan ya bijiro da ita.

A jerin sakonninsa a shafin Tuwita, Salkida ya ce, "a cikin tattausar murya, sabanin yadda ya saba magana cikin zafi, Shekau ya bayyana cewa yanzu suka fara yaki. Ya ci al washin cewa mayakan kungiyarsa ba zasu ajiye makamansu ba tare da zargin gwamnan da fassara ayar Qur'ani ba daidai ba."

Shekau ya mayar wa da gwamna Zulum martani, ya zarge shi da rashin sanin Al-Qur'ani
Gwamnan jihar Borno; Farfesa Babagana Zulum
Asali: Twitter

Da yake magana a kan mayakan kungiyar da kan iya ajiye makamansu, Shekau ya ce, "ya kamata su sani cewa wannan aiki ne na Allah, ba aikin wani mutum ba."

DUBA WANNAN: Boko Haram suna can suna kashe jama'a, kuna nan kuna karbar N1,000 a kan titi - Sojoji sun fusata Zulum

Amma wasu masu nazari da hasashen al'amura sun bayyana musayar yawu a tsakanin Shekau da Zulum a matsayin babbar nasara a matakan yin sulhu da 'yan ta'adda a kowanne mataki.

Tun cikin shekarar 2009 jihar Borno da wasu jihohin yankin arewa maso gabas ke fama da hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba miliyoyin jama'a da muhallinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel