Tashin hankali: An kama saurayi da yake zuwa ya kwanta da uwa da kuma 'ya'yanta mata guda biyu

Tashin hankali: An kama saurayi da yake zuwa ya kwanta da uwa da kuma 'ya'yanta mata guda biyu

- Wani mutum mai suna Adesiyan ya shiga hannun 'yan sanda sakamakon yaudarar wata mai takaba da yaran ta mata biyu

- Adesiyan na lalata da uwa ne da kuma yaranta mata biyu masu shekaru 13 da 19

- Ya shiga hannun 'yan sanda ne bayan da yaje sace yaran mata biyu gudun su bada shaida a kan shi

Wani mutum mai suna Adesiyan amma anfi sanin shi da Oba, ya shiga hannun 'yan sanda saboda yaudarar wata mai takaba da yayi. Yana kwanciya da ita tare da 'ya'yanta biyu.

Adesiyan ya yaudari mai takabar zuwa muguwar hanyar a kan cewa zai tallafawa gidanta don yana gab da wargajewa.

Mai takabar ta fara samun matsala da Adesiyan ne bayan da ya fara kwanciya da 'yarta mai shekaru 19 da dayar mai shekaru 13. Ya ce maganin da yake musu dole ne a tsaftace gabansu da farko ta hanyar amfani da farin kyalle.

Shugaban kungiyar mutanen Odua dake yankin tashar Iju a jihar Legas ya shiga fadan bayan da mai takabar ta ga ba zata iya zama yana lalata da ita da yaran ta ba.

Fakorede Oluifa, shugaban kungiyar jama'ar Odua din ya ce: "Bayan kwanaki hudu, na samu Olanike da Adesiyan suna fada saboda yana lalata da yaran ta mata biyu. A nan ne take sanar dani cewa yana lalata da 'yan matan biyu da ikirarin cewa zai warkar da danta daga mugun ciwon da ya kwantar dashi."

KU KARANTA: Cudanya da 'yan Nollywood ba komai bane illa cigaba ga 'yan Kannywood - Hadiza Muhammad

Shugaban ya cigaba da bayyana yadda suka so kai Adesiyan gaban hukuma amma sai ya gudu. Amma kuma, washegari sai ya koma gidan da niyyar sace 'yanmatan biyu ta yadda ba zasu bada shaida a kan shi ba.

Duk da kuwa kafin nan 'yanmatan sun yi bayanin yadda yake kwanciya dasu kuma ya goge gabansu da farin kyalle, a cewar shi na magani ne.

Bayan shigar Adesiyan hannu, ya ce ya fara kwanciya da yaran ne da yardar mahaifiyarsu don kawo karshen ciwon danta namiji tilo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel