Cudanya da 'yan Nollywood ba komai bane illa cigaba ga 'yan Kannywood - Hadiza Muhammad

Cudanya da 'yan Nollywood ba komai bane illa cigaba ga 'yan Kannywood - Hadiza Muhammad

- Sananniyar jaruma Hadiza Muhammad tace cigaban masana'antar Kannywood ce da arewa idan jarumai na hadewa da na Nollywood

- Ta bayyana cewa, ta samu dama a kwanakin baya na shiga Nollywood din amma wasu dalilai ne suka hanata

- Jarumar tace, a kan batun kasuwancin kannywood, masu downloading ne ke matukar kawo musu tsaiko da kashe kasuwa

Fitacciyar jarumar Kannywood Hadiza Muhammad wadda aka fi sa ni da Hadizan Saima ta tabbatar cewar a kwanakin baya ta samu gayyata zuwa kudancin kasar nan domin shiga fim din Nollywood.

Jaruma Hadiza Muhammad ta bayyana hakan ne yayın da aka gudanar da taron karrama jaruman Kannywood din na Bon Award wanda ya gudana a jihar Kano a kwanakin baya.

Hadiza ta ce "wasu dalilai ne kawai suka kawo tsaiko na rashin shiga fim din Nollywood din.

"Duk inda al'umma ta ke a rabe to akwai wasu abubuwa da ba za a iya cin musu ba, amma idan a ka ce an samu hadin kai to babu shakka za'a cimma nasarar da a ke bukata a kowanne bangare".

Ta kara da cewa "Arewacin Najeriya muke gudanar da sana'ar mu ta fim, su kuma suna kudancin kasar nan su na gudanar da sana'ar su ta fim, kuma su na amfani da harshen turanсi da kuma yarensu wanda hakan akwai banbancin yare da al'ada a tsakanin mu. Hada kai da mu ke yi a halin yanzu na fina-finai ya na da amfani matuka domin ta hakan ne zamu yi fim ya kuma je inda ba a tsammani a fadin duniyar nan.

KU KARANTA: Musulunci ya samu karuwa: Manyan Fastoci guda biyu a jihar Ogun sun dawo addinin Musulunci

"Ba wani abu ba ne in mun hadu da jaruman kudancin kasar nan a harkar fim, domin ta wannan hanyar ce za mu iya karuwa a tsakanin juna. Saboda haka har idan mun hadu da jaruman kudancin kasar nan mun yi cudanya da juna, zamu samu cigaba kuma fim din mu zai je inda ba'a tsammani". In ji Jarumar

Jarumar ta kuma rufe jawabin ta ne da cewar "ba wani abu bane samun damar, kawai dai wasu dalilai ne suka hana ni, saboda a kwanakin baya an yi mun tayi amma ban samu damar zuwa ba don na yi fim din Nollywood, kuma batun kasuwan cin mu na Kannywood kuwa, ba wani abu bane yake kawo mana tsaiko, illa kawai masu harkar tura fim a waya wato 'yan downloading ne suke mayar da hannun agogo baya a harkar masana'antar Kannywood". A cewar Hadiza Muhammad.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel