Musulunci ya samu karuwa: Manyan Fastoci guda biyu a jihar Ogun sun dawo addinin Musulunci
- Shiriya daga Allah take kuma shi ke shiryarwa ko batarwa
- Wasu fastoci biyu a jihar Ogun sun mika kansu ga Allah tare da karbar musulunci
- A bidiyon, an ga yadda suka je gaban malami tare da jaddada cewa babu wanda ya tirsasa su zuwa karbar musulunci
Wasu fastoci guda biyu a jihar Ogun sun karba musulunci.
Kamar yadda Kiristoci ke yada addinin Kirista, kuma a rungumeshi, haka musulmai ke yi ba tare da sassautawa ba. A hakan kuwa kowanne lokaci ake samun wadanda ke sauya addinin da suke bi da farko zuwa wani daban.
Wani bidiyon dake yawo a kafar sada zumuntar zamani ya jawo cece-kuce. Bidiyon na dauke da fastoci biyu ne da suka je wajen wani wa'azi a jihar Ogun har suka mika wuya ga musulunci tare da karbar kalmar Allah.
A bidiyon, mutumin dake tsaye a matsayin malamin yayi musu magana da harshen yarbanci. "Dukkanku biyun da kanku kuma tare da ra'ayin kanku kuka zo don karbar musulunci. Kuma babu wanda ya tilasta ku".
KU KARANTA: Yayin da ake jana'izar Kwamandan Iran, an kai mummunan hari Baghdad babban birnin Iraqi
Daga bisani, a bidiyon an bayyana yadda suka karba musulunci a matsayin sabon addininsu kuma da yadda suka fada matukar farin ciki bayan yin hakan.
Rahotanni daga Ogun sun nuna cewa, sabbin sunansu shine Muhammad Saheed da Muhammad Jamiu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng