Boko Haram: Gwamna Zulum ya fusata, ya gargadi sojoji a kan abinda suke yi wa Jama'a
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya zargi sojoji da karbar N1000 daga matafiya
- Ya yi wannan zargin ne a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu a yayin da ya ziyarci babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
- Zulum yace jami’an tsaron na karbar N1000 ne daga matafiyan da suka kasa bayyana katin shaidarsu
Sojojin dake gadin shingayen kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri sun fusata gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum da yammacin ranar Litinin.
Ran gwamna Zulum ya baci ne yayin da yaci karo da dogon layin ababen hawa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Jakana, garin da ‘yan Boko Haram suka kai hari a ranar Asabar.
Gwamnan, wanda ga bisa dukkan alamu yana da labarin halayyar sojojin da suke tsayawa a shingayen kan hanyar, ya sauko daga motar da yake ciki tare da nufar wurin da sojojin da suka haddasa cunkosun ke tsaye.
DUBA WANNAN: Fizgen waya: Yadda jama'a suka taimakawa 'yan sanda wajen cafke barawo
“Zan shigar da korafi a kan dukkaninku dake aiki a nan wurin don ba zamu yadda da abun da kuke aikatawa ba. Mayakan kungiyar Boko Haram suna can suna kaiwa jama’a hari, ku kuma kuna nan kuna karbar N1000 a kan kowacce mota,” a cewar gwamna Zulum.
Daya daga cikin sojojin ya kokarta wajen kwantarwa gwamnan da hankali, amma hakan bata yuwa ba saboda fusatar da gwamnan yayi.
Kalli bidiyo a kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng