Ba zamu amince da karin kudin wutar lantarki ga yan Najeriya ba – PDP ga Buhari

Ba zamu amince da karin kudin wutar lantarki ga yan Najeriya ba – PDP ga Buhari

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sanar da rashin amincewarta da karin farashin wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi, sa’annan ta yi tir tare da Allah wadai da wannan manufa na gwamnatin tarayya.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito PDP ta bayyana haka ne ta wani rubutu da ta yi a shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda ta bayyana karin a matsayin matakin kuntata ma yan Najeriya, don haka ta yi kira ga gwamnati ta janye karin.

KU KARANTA: Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

“PDP ba ta amince da karin farashin wutar lantarki da gwamnatin APC ta yi ga yan Najeriya da kashi 200 ba, kuma mun yi watsi da shi tare da tofin Allah tsine a kan haka. Wannan mataki bai dace ba, kuma zai kara tsunduma yan Najeriya cikin halin matsi da suke ciki.

“Don haka muke kira ga gwamanti ta gaggauta janye matakin, sa’annan muna shawartar ta ta cigaba da tattaunawa da yan Najeriya kafin ta cimma wannan matsaya. Abin takaic ne a ce yan Najeriya da a yanzu suke fama da karin haraji da APCta kakaba musu, kuma an kara tsawwala musu da karin kudin wuta.

“A fahimtarmu, karin farashin lantarkin a wannan halin matsalin tattalin arziki da ake ciki zai illata yan Najeriya, kuma zai sa farashin kayayyakin masarufi su tashi, musamman kudin haya, ilimi, kiwon lafiya, abinci da sauransu. ” Inji PDP.

Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar kula da kamfanonin wutar lantarki, NERC, ta amince da karin farashin wutar lantarki ga yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel