Yayin da ake jana'izar Kwamandan Iran, an kai mummunan hari Baghdad babban birnin Iraqi

Yayin da ake jana'izar Kwamandan Iran, an kai mummunan hari Baghdad babban birnin Iraqi

- Sabon rahoto daga gidan talabijin na CNN ya bayyana cewa an samu sabon hari a birnin Baghdad

- Wannan sabon harin ya biyo bayan wani harin da yayi sanadin mutuwar mataimakin shugaban PMF

- Daga bisani an gano cewa kasar Amurka ce ta kara kai harin kuma da niyyar samun PMF

Kamar yadda rahoton CNN ya bayyana, an kara samun wani harin a birnin Baghdad, babban birnin kasar Iraq. Wannan sabon harin ya kashe mutane tare da raunata wasu da dama.

Kamfanin labaran ya bayyana cewa, a harin da aka kara kaiwa, an so samun tawagar wasu manyan ‘yan kungiyar tsageru 40 ta musulmai ‘yan Shi’a.

“Rahoton farko ya bayyana cewa harin ya so samun wata tawagar masana kiwon lafiya ne dake kusa da filin wasa nan a Taji dake Baghdad,” cewar wata sananniyar kungiyar soji.

KU KARANTA: Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Landan

Wannan ya biyo bayan harin da kasar Amurka ta kai wanda yayi sanadin mutuwar mataimakin shugaban PMF, Qassem Soleimani.

Duk da dai a halin yanzu ba a danganta wannan sabon hari da Amurka ba, wani rahoto da gidan Talabijin na Iraq ya bayyana, yace kasar Amurka ce ta sake yi.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan kasar Amurka ta bayyana daukar alhakin kisan babban kwamandan yakin kasar Iran a jiya, bayan ta kai musu hari kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel