Rusau a Zaria: Damuwa da kunci yayin da gwamnati ta rushe kasuwanni

Rusau a Zaria: Damuwa da kunci yayin da gwamnati ta rushe kasuwanni

Rushe kasuwannin Dan Magaji da Sabon Gari a birnin Zazzau ya jawo wa 'yan kasuwa da wadanda suka dogara dasu tsananin kunci da tashin hankali. Hakan kuwa ya jefa su cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda da yawansu suka sanar.

Daruruwan 'yan kasuwa sun shiga halin kaka-ni-kayi da wannan rusau din saboda an barsu babu tsuntsu balle tarko. A halin yanzu suna ta zaman rashin abin yi saboda ba a basu wasu shagunan ko yankin da zasu zuba kayansu don cigaba da sana'arsu ba.

A tattaunawar da jaridar Daily Trust tayi da wasu daga cikin 'yan kasuwar, sunyi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta dube su tare da kirkiro musu da hanyar da zasu kawo karshen wannan halin da suka fada na rashin sana'a.

An gano cewa, tuni ake ta kokarin gyaran kasuwannin, amma ba a mayar da hankali ba har sai zuwa lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Alhaji Namadi Sambo.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da tagwaye mata a Katsina

A wancan lokacin ne, wasu daga cikin kadarorin gine-gine na 'yan kasuwar sun koma hannun gwamnatin jihar bayan da suka mayar wa da 'yan kasuwar kudinsu. Gwamnati sai ta damka su hannun karamar hukumar.

Gidajen dake tsakiyar kasuwa an karbesu a wancan lokacin tare da biyan masu su. Amma daga bisani, gwamnatin karamar hukumar ta sake siyar da wadannan kadarorin ga 'yan kasuwa. A halin yanzu kuwa da aka fara rusau din, 'yan kasuwar na ta koke tare da korafin cewa gwamnatin jihar bata biya su hakkokinsu na miliyoyin nairori ba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bankado, wasu daga cikin 'yan kasuwar dake koke sun tura kudin siyan shagunan ne ta wani asusu da ba na gwamnati ba. Wasu daga ciki kuwa hannu da hannu suka bada kudin siyen shagunan, ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari na wancan lokacin.

A lokacin da aka sanar da 'yan kasuwar cewa za a rushe kasuwar da gaggawa, ya bayyana cewa basu da wata kwakwarar shaida a hannu dake nuna cewa wadannan shagunan mallakinsu ne.

Daya daga cikin mamallakan rukunin shaguna a kasuwar ya ce, "A tunaninku hauka muke da zamu gina shaguna a kasuwa ba tare da wata shaida ba? A lokacin da dan aiken shugaban karamar hukumar ya bukaci in bada kudina a hannu, ban bada ba. Sai nace zan zuba a asusun banki. A halin yanzu da ya musanta hakan, an binciki tarihin shige da ficen kudi na asusun bankinsa kuma an gani. Adon haka muke bukatar tallafin hukumar EFCC."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel