Yadda ake kai 'yan acaba cikin makabarta ana basu wajen kwana a ciki a birnin Abuja

Yadda ake kai 'yan acaba cikin makabarta ana basu wajen kwana a ciki a birnin Abuja

- Babban Limamin Kubwa a Abuja, ya bayyana amfanin ba ‘yan achaba masauki a makabartar yankin

- Ya bayyana cewa, suna taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro a makabartar saboda aiyukan miyagu da ya yawaita

- Limamin yayi kira ga masu hannu da shuni a kan su dinga kai ziyara tare da tallafi ga makabartu

Babban Limamin Kubwa a Abuja, Malam Abdurrahim Yahaya Muhammad ya ce masaukin da suka ba wa wasu masu sana’ar achaba a makarbarta a garin, ya matukar taimakawa wajen jaddada tsaro da kuma magance kutsen da wasu matsafa keyi a makabarta.

Jaridar Aminiya ta tattauna da malamin ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan aikin gayya, da ya hada da yankar ciyawa da cike kaburbura da aka gudanar a makabartar.

Ya ce ko a watanni biyu da suka gabata an samu wani malami da yaje makabartar da wasu da ba musulmai ba suka tone wani kabari tare da saka layu. Ya ce wani manomi dake da gona kusa da makabartar ne ya gansu kuma ya sanar da ‘yan achaban ta waya, inda suka cafke mutanen da wanda ya sa su wannan mummunan aikin.

“Bayan da ‘yan achaban suka kamashi ne, muka dauke shi a mota tare da mika shi ga ‘yan sanda,” cewar Liman.

Zamansu a wajen na taimaka wa har ga wannan unguwar kuma suna taimakawa wajen gyaran makabartar.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari zai bar ofis kafin karshen 2020, sanadiyyar tsige shi da za ayi - Fasto

Malam Abdurrahim ya bukaci musulmai a duk inda suke da su dinga taimakawa wajen gyara makabarta akai-akai. Ya kara da kira ga masu hannu da shuni da su dinga ziyartar makabartu don ganin halin da suke ciki ko akwai bukatar tallafi.

Mai gadin makabartar, Malam Ibrahim Salihu ya ce sakamakon yadda wasu bata gari ke miyagun aiyuka a makabartu, yasa basu barin mutane ziyara sai an bi su tare da saka musu ido.

”Akwai wani mai hannu da shuni da yazo da rago a kan zai yanka tare da bada sadaka, amma zai saka kan da kafafuwan a cikin kabarin dan uwanshi. Bamu yadda da hakan ba gaskiya. Ya kara da cewa zai hada mana da kudi, amma muka ki.” Cewar mai gadin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel