Kisan kwamandan Sojan Iran: Ayatollahi Khameini ya sanar da sabon babban kwamanda

Kisan kwamandan Sojan Iran: Ayatollahi Khameini ya sanar da sabon babban kwamanda

Jagoran gwamnatin kasar Iran, Ayatollah Ali Khameini ya sanar da nadin Birgediya Janar Esmail Ghaani a matsayin magajin Janar Qassem Soleimani, babban kwamandan rundunar Quds na Sojojin juyin juya hali da kasar Amurka ta kashe.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito jagoran na Iran yace duk wasu tsare tsare da rundunar ta yi a baya ba za su canza ba duk da mutuwar Janar Qassem, domin kuwa magajinsa zai daura ne daga ina ya tsaya.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Ka gama rawar, za mu hadu a kotu – Magu ga Fayose

Kisan kwamandan Sojan Iran: Ayatollahi Khameini ya sanar da sabon babban kwamanda
Ayatollahi Khameini da Ghaani
Asali: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ruwaito marigayi Qassem shi ne babban kwamandan Sojojin Quds, wani bangare daga rundunar Sojojin juyin juya hali na kasar Iran, wanda ke kula da duk wani aikin Soji na kasar Iran a kasashen waje, musamman yake yake.

A ranar Juma’a ne Amurka ta kashe Janar Qasseem ta hanyar amfani da wani jirgi mai sarrafa kansa daya yi masa luguden bama bamai yayin da yake cikin ayarin motoci a kan hanyarsa ta zuwa filin sauka da tasin jirage ma Baghdad.

Harin ya rutsa da Qasseem da mataimakin shugaban Sojojin yan shia na Hashd Shaabi, Abu Mahdi Al-Mohandes da wasu manyan Sojojin kasar Iran guda 25. Haka zalika jim kadan bayan wannan hari, Sojojin Amurka sun kashe Mohammed Reda Al-Jaberi, mai magana da yawun Sojojin Shia da jami’ansa 5.

Jami’an rundunar Sojan Iraq sun tabbatar da kisan Qasseem, inda suka ce sun hangi saukar rokokin bamabamai guda uku a kan wasu ayarin motoci guda biyu, wanda suka kashe mutane da dama dake yankin.

Sai dai gwamnatin kasar Amurka ta sanar da daukan alhakin kisan Janar Qassem Soleimani, inda tace ta kashe shi ne a wani mataki na ‘kare kai’, kamar yadda shelkwatar tsaro ta kasar, Pentagon ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel