Tsananin sanyi ya hana mutane fita aiki a garin Jos

Tsananin sanyi ya hana mutane fita aiki a garin Jos

- Mazauna birnin Kano da Jos sun koka da tsananin sanyin da wannan canjin yanayin ya zo dashi

- A daren Laraba ne aka auna tare da gano cewa sanyin Kano ya a ma'aunin selsus ya kai 7 inda na Jos ya kai 11

- Wannan lamarin kuwa ya hana magidanta tare da masu sana'o'i fitowa don cigaba da lamurran rayuwarsu

Mazauna Kano da Jos sun kasance a cikin gidajensu bayan sanyin da ya ta'azzara a wannan yanayin da ya sauya.

Sauyin yanayin yasa mutane kan saka manyan rigunan sanyi don kare kansu daga sabon yanayin. Yanayin yasa mutane sun koma amfani da gawayi ko itace don samun dumin da suke bukata.

A sa'o'in farko na jiya ne aka samu tsananin sanyin da yasa masu adaidaita kammaluwa a cikin gida.

Mazaunin garin, Malam Bello Sani, yace bai iya fita da safe ba kamar yadda ya saba saboda tsananin sanyin garin.

Kamar yadda yace, birnin Kano sanyinshi ya kai ma'aunin selsus 7 a daren Laraba wanda hakan yafi birnin London dake da ma'aunin selsus 9 a wannan daren.

"Dole ne in siyo gawayi a kasuwar Sabon Gari wanda ni da iyalina zamuyi amfani dashi don dumama jikinmu," in ji shi.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Bashi Muhammad, yace ya kasa tuka babur din shi saboda tsananin sanyin garin.

"Munyi sa'a da ake hutun makaranta amma da ba zai yuwu mu kai yaranmu makaranta ba," in ji shi.

KU KARANTA: Na shiga karuwanci ne saboda ita ka dai ce hanyar da zan iya samun kudi - Facardi

Hakazalika, mazauna garin Jos suna kokawa a kan tsananin sanyin da suke fama dashi a garin. Sun bayyana cewa sanyin na hana su aiyukan rayuwarsu.

Dumin garin har ya kai ma'aunin selsus 11 da yammaci amma ya kai 19 da rana.

Wasu daga cikin mazauna garin sun koka a kan irin sanyin don basu fitowa kwata-kwata waje.

John Emeka dalibi ne wanda ya koka da wahalar da yake sha kafin ya fito daga daki saboda tsananin sanyi.

"Kamar yadda kuke gani, ina sanye ne da babbar rigar sanyi da kuma hula, safar kafa da ta hannu, duk don in samu dumi." Cewar Emeka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel