Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da tagwaye mata a Katsina

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da tagwaye mata a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun sace wasu ‘yan biyu a kauyen Gizawa dake karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina. An gano cewa ‘yan bindigar sun hari garin ne a sa’o’in farko na jiya a lokacin da mazauna garin ke bacci.

Majiyoyi da dama sun ce masu garkuwa da mutanen sun fito da Hassan da Hussaina Idris ta karfin tsiya daga dakunansu.

Hakazalika, an gano cewa wasu ‘yan bindiga sun hari gidan wani Magaji Abu a kauyen Badole, inda suka yi awon gaba da shanayensa.

‘Yan sanda dai basu mayar da martani ba a kan tambayoyin da aka yi musu kafin a rubuta wannan rahoton, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu, mutane shida ne suka kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar a ranar farko na sabuwar shekara, bayan ruwan wuta da ya wanzu tsakanin masu garkuwa da mutanen da ‘yan sanda.

DUBA WANNAN: Jiragen ruwa 18 makare da man fetur da kayan abinci suna hanyar zuwa Najeriya - NPA

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah yace, “A ranar 1 ga watan Janairu 2020, wajen karfe 12:30 jami’an suka samu kiran gaggawa. Wasu ‘yan bindigar da suka ki tuba sun kwashe mata a wata gona dake kauyen Mata-Mulki dake karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.”

“Runduna ta musamman wacce ta samu jagoranci DPO din Batsarin ta gaggauta isa yankin. Kungiyar ta fatattaki bata garin har cikin daji inda suka yi ruwan wuta,” in ji ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa ‘yan bindigar sun aje makamansu inda suka tsere zuwa cikin dajin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel