Yaki da rashawa: Ka gama rawar, za mu hadu a kotu – Magu ga Fayose
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya mayar da martani game da bidiyon dake yawo a kafafen sadarwar zamani inda aka hangi tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayo Fayose yana tikar rawa da wata baturiya duk da cewa EFCC na tuhumarsa a satar kudin jama’a.
Premium Times ta ruwaito Magu ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Tony Amokeodo wanda ya tattauna da majiyar Legit.ng ta wayar tarho inda yace hukumar ta riga ta shigar da Fayose kara gaban kotu, don haka ba ta da cewa game da wannan bidiyon har sai ya dawo Najeriya an cigaba da shari’ar.
KU KARANTA: Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria
“Ba zamu yi wani magana game da wannan bidiyo ba, saboda kararsa muke yi a kotu ba wai cin zalinsa ba, baya ga haka, kotu ce ta ba shi daman fita kasar waje saboda rashin lafiya. Abin da muka sani kawai shi ne dole ne tsohon gwamnan zai dawo ya cigaba da halartar zaman kotun, tabbas zamu hadu da shi a zama na gaba.” Inji shi.
Hukumar EFCC na tuhumar Fayose da laifin satar kudi naira biliyan 2.2, amma a ranar shiga sabuwar shekara an hange shi yana rawa da wata baturiya a kasar waje tare da zuwa bakin tafki yana shakatawa a kasar Caribbean Islands.
Wadannan hotuna suka sa yan Najeriya suke kallon kamar Fayose ya yaudari kotu ne, inda ya yi mata karyar ba shi da lafiya yana neman ta bashi daman fita duba lafiyarsa, amma sai ga shi ya buge da yawn nishadi.
Sai dai a wani martani da Fayose ya mayar ta shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, ya yi kira ga duk masu sa masa ido dasu shiga taitayinsu, domin kuwa ba zai daina kuntata musu rai ba, kuma duk wanda ya ji haushi ya rungumi turansifoma.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng