Tirkashi: Mata ta sayar da mijinta sukutum akan N6,000, ta siyawa 'ya'yanta kayan sawa

Tirkashi: Mata ta sayar da mijinta sukutum akan N6,000, ta siyawa 'ya'yanta kayan sawa

- Wata mata 'yar asalin kasar Kenya mai suna Edna Mukwana ta ba mutane matukar mamaki

- Mukwana ta siyar da mijinta a kan naira dubu shida don ta siya wa yaranta sabbin kayan sabuwar shekara

- Dalilinta kuwa shine don ta kama mijin nata dare-dare kan karuwa a kan gadon aurensu

Wata mata 'yar asalin kasar Kenya mai suna Edna Mukwana ta ba mutane da yawa mamaki. Mukwana ta siyar da mijinta ne a kan naira dubu shida kacal don ta samu kudin siya wa 'ya'yanta sabbin kayan sabuwar shekara.

Kamar yadda Mukwana ta sanar, ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta kama mijinta dumu-dumu da wata mata daban a kan gadon aurensu. Mai gidan nata ya aikata hakan ne bayan da yayi kwanaki bakwai bai waiwayo su gida ba.

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya dirkawa kawarta ciki kwana hudu da zuwanta gidansu

Tace, "Mijina ya auri giya da kuma karuwai kala-kala. Nace wa matar da ke batar dashi da ta turo min wasu kudi don in bar mata shi, amma sai ta turo dubu shida kacal. Nayi amfani da dukkan kudin ne don siya wa 'ya'yana sabbin kaya don sabuwar shekara."

Da aka tambayi Mukwana ko zata kara karbar mijin nata, sai ta ce, "A'a sam. Bana bukatar shiga sabuwar shekara da matsalar 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel