Ma'aikata sun harbe wasu Zakuna uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum

Ma'aikata sun harbe wasu Zakuna uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum

Ma'aikatan hukumar raya gandun daji a kasar Amurka sun harbe wasu Zakunan kan tsauni guda uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum da suka samu a kusa da wani tsauni da masu yawon bude ido ke yawan ziyarta a jihar Arizona.

Wani jami'in dan sanda a yankin Pima ya ce sun samu ragowar gawar wani mutum a kusa da tsaunin dake arewacin Tucson a ranar Talata.

A ranar Laraba ne sashen raya gandun daji da kifaye a Arizona ya sanar da cewa an harbe zakunan guda da daddare.

Duk da ba a zargin cewa Zakunan suna kashe mutane, an samu ragowar sassan jikin mutum a muhallinsu.

"Duk da zamu gudanar da bincike a kan gawar da mutumin, bamu yarda cewa Zakunan ne suka kashe shi ba. Mun fi gamsuwa cewa sun yi kalaci da gawar mutumin ne bayan mutuwarsa," a cewar kakakin hukumar raya ganduje da Kifaye, Mark Hart, yayin ganawarsa da wani gidan Talabijin.

Hukumar ta kara da cewa halayyar da Zakunan suka nuna zata iya basu kwarin gwuiwar fara haike wa mutane tare da kashesu a nan gaba, wanda hakan zai mayar dasu masu hatsari ga dumbin jama'ar dake ziyartar tsaunin domin yawon bude ido.

A kalla akwai kimanin Zakuna 2,000 zuwa 2,7000 a tsaunikan daban - daban dake jihar Arizona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel