Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da sansanin kungiyar ta’addan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da sansanin kungiyar ta’addan Boko Haram

Dakarun sojan saman Najeriya sun sake samun nasarar yin watsa watsa da dimbin mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Harama a wani samame da suka kai musu ta sama ta hanyar amfani da jiragen yaki.

Daily Trust ta ruwaito zaratan Sojojin rundunar sojan saman sun kaddamar da hari a kan yan ta’addan ne a wani sansaninsu dake kauyen Abulam dake cikin dajin Sambisa a jahar Borno, inda suka kashe yan ta’addan tare da lalata sansanin.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige mutane 4 har lahira a babban birnin tarayya Abuja

Mai magana da yawun rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ya bayyana cewa dakarun rundunar sun kaddamar da hare haren ne a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2019 a matsayin fara aiki na musamman mai taken “Operational Rattle Snake 2”

Daramola yace rundunar ta zabi Abullam ne domin kaddamar da harin bayan samun bayanan sirri dake nuna cewa yan ta’addan sun cigaba da taruwa a sansaninsu dake Abullam bayan daukan tsawon lokaci basa amfani da shi.

Da wannan ne dakarun rundunar suka dauki matakin ragargaza sansanin da nufin karya lagon yan ta’addan ta hanyar amfani da jiragen yaki da zasu yi ruwan wuta a sansanonin ta yadda za’a halaka yan ta’adda tare da lalata kayan aikinsu.

“Ba tare da bata lokaci ba muka tura jiragen yakinmu tare da jiragen leken asiri domin tabbatar da mun samu wuraren da muke hari yadda ya kamata, cikin kwarewa jiragen mu suka yi ma sansanin luguden wuta, wanda yayi sanadiyar tashin sansanin gaba daya daga aiki tare da kashe yan ta’adda da dama.” Inji shi.

Daga karshe Daramola yace a tsakiyar watan Disambar 2019 rundunar Sojan sama ta tsara aikin Operation Rattale Snake 1, kuma ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da shi, don haka ta bullo da Operation Rattle Snake 2 domin daurawa daga inda aka tsaya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel