Bani da wata matsala da Ganduje - Abdulmumin Jibril

Bani da wata matsala da Ganduje - Abdulmumin Jibril

Abdulmumin Jibril, wanda za a maimaita zabensu a ranar 25 ga watan Janairu, na kujerar majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, ya ce shekarar da ta gabata ta kasance mai kyau ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jibril, wanda ya zanta da manema labaran gidan gwamnati a Abuja bayan ganawa da yayi da Shugaba Buhari a ranar Talata, yace nasarorin da aka samu a bangaren noma da kiwo, tattalin arziki, habaka ababen more rayuwa, yaki da rashawa da tsaro, dole ne a cigaba da kiyayesu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Na tattauna da shugaban kasa ne a kan cigaban da aka samu a shekarar nan, don in jinjina masa cigaban da muka samu a fannin tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma tsaro a kasar nan. Sannan kuma mun duba lamurrran da suka danganci habaka ababen more rayuwa a fadin kasar nan da bukatar kiyayesu.” Ya ce.

DUBA WANNAN: DPR ta rufe gidajen mai 10 a Kaduna

Ya kara da cewa, “A bangaren gyaran fannin aikin gona, akwai bukatar mu kiyaye. Yaki da ta’addanci da kuma nasarorin da aka samu, tsananin fahimtar juna dake tsakanin shuwagabanni shima abun alfahari ne.”

“A takaice dai, wannan shekarar tazo da tarin abubuwa masu amfani ga shugaban kasa da kuma gwamnati kuma ina tunanin wajibi ne garemu da mu jinjina musu. Abinda muka tattauna kenan, a takaice.” Cewar Jibrin.

A lokacin da aka tuntube shi a kan cewa wasu a jihar Kano basa goyon bayan komen sa zuwa majalisar, Jibrin ya ce, “Wannan ba gaskiya bane. Jita-jita ce dai kamar yadda suka saba, muna kuma kokari tare. Ina da tabbacin akwai nasara a sake zaben da za a yi, ba wai a Kano ba kadai, ga APC duk fadin kasar nan inda za a sake zabe a ranar 25 ga wata.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel