Gwamnan jihar Zamfara ya ware Naira Biliyan Daya domin gyaran Masallatai da Makabartu a jiharsa

Gwamnan jihar Zamfara ya ware Naira Biliyan Daya domin gyaran Masallatai da Makabartu a jiharsa

- Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan daya don gina masallatai, gyaran makabartu da ciyarwar watan azumi a 2020

- Kwamishinan al'amuran addinin musulunci na jihar ya bayyana cewa dama wannan al'adar jihar ce amma zasu yi gyara tare da sauya salonta

- Za a gina masallatai a kowacce masarauta cikin guda 17 dake jihar tare da gina cibiyar ilimin addinin Islama uku a fadin jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware makuden kudi har naira biliyan daya don gina masallatai da kuma gyara makabartu.

Gwamnatin jihar ce ta tabbatar da ware wannan kudin don gina masallatan Juma'a, gyaran makabartu, kayan azumi da sauran lamurran addini a jihar a shekarar 2020.

Kamar yadda rahoton jaridar Independent Nigeria ta ruwaito, kwamishinan al'amuran addinin musulunci na jihar, Sheikh Tukur Jangebe ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kudin ma'aikatarshi a gaban majalisar jihar a Gusau a ranar Talata.

Jangebe ya tabbatar da cewa, naira miliyan 300 daga cikin wannan kudin za a yi amfani dasu ne wajen tallafawa 'yan kauye da kayan azumi na watan Ramadan a shekarar 2020. "Tun farko dama a kowanne watan Ramadan, gwamnatin jihar na kafa cibiyoyin ciyarwa a fadin jihar karkashin ma'aikatar.

KU KARANTA: A karon farko an samu jaruma bakar fata da ta fara fitowa a fim din Indiya

"A wannan shekarar, zamu gyara ciyarwar da ake a lokacin azumin a jihar. Zamu tabbatar da ta isa har yankunan karkara. Mun shirya samar da gero da abubuwan bukata masu matukar amfani ga marasa karfi a maimakon kafa cibiyoyin ciyarwa din", cewar Kwamishinan.

Kamar yadda yace, a karkashin kasafin kudin wannan shekarar, ma'aikatar zata gina masallatan Juma'a a masarautu 17 na jihar.

"Zamu gina cibiyar musulunci daya a kowanne yanki cikin yankuna uku na sanatoci da muke dasu a jihar." In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel