Innalillahi: Dan kwallon Najeriya ya bayyana yadda ya kashe kanwarsa yayin da take dauke da tsohon ciki

Innalillahi: Dan kwallon Najeriya ya bayyana yadda ya kashe kanwarsa yayin da take dauke da tsohon ciki

- Tsohon dan wasan kwallon kafar jami'ar Texas, Michael Egwuagu na hannun 'yan sanda

- Sun kama shi ne sakamakon zarginshi da ake da kisan yayarshi mai dauke da juna biyu

- Ya soke ta ne da wuka a wurare da dama bayan hatsaniya ta hada ta dashi, inda ajali ya kaita har lahira

An zargi tsohon dan kwallon kafar jami'ar Texas, Michael Egwuagu da kashe 'yar uwarshi a ranar Juma'a. Ya amsa laifinshi a wani faifan sautin muryar bayan mutuwar Jennifer Ebichi, kamar yadda 'yan sanda suka sanar.

"Na kashe Jennifer," Michael mai shekaru 25 ya ce kamar yadda naurar daukar sautin dake jikin kofar gidan Ebichi ta nade.

Jennifer mai shekaru 32 na da cikin wata uku a jikinta. Martin Egwuagu, babban yayan Michael ya sanar da 'yan sanda cewa ya samu sakon Jennifer ne wajen karfe 5:30 na asuba a ranar Juma'a. Ta bayyana cewa tana tare da Michael kuma suna hatsaniya. Martin yayi magana da Michael don kwantar mishi da hankali amma sai yaji yana ta wasu maganganu marasa dadin ji.

KU KARANTA: Uwa da 'Ya sun sheka barzahu bayan fasto ya basu jikon magani sun sha

Ya bayyana cewa, wajen karfe 4:10 na yamma ne yaje gidan Jennifer ya tarar da wata mata a kofar shiga. Bayan nan ya ga Jennifer kwance cikin jini a kichin tare da shaidar sukarta da aka yi a wurare daban-daban. Daga nan ya tarar da Michael a tsakar titi durkushe kamar mai addu'a.

A halin yanzu Michael Egwuagu yana gidan yari na Travis County tun a ranar Lahadi. An shirya kudin belinshi a $500,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng