Kannywood: Manyan nasarori 5 da masana'antar ta samu a 2019

Kannywood: Manyan nasarori 5 da masana'antar ta samu a 2019

A shekarar 2019 an samu manyan nasarori a masana'antar fina-finan Hausa. Wasu 'yan wasan kwaikwayon sun samu manyan nasarori tare da jinjina a cikin gida Najeriya da wajen kasar sakamakon arwar da suke takawa a masana'antar.

Jaridar Premium Times ta tattara wasu nasarorin da aka samu a masana'antar a 2019.

1. Zango ya biya naira miliyan 47 don daukar nauyin marayu 101 a makarantar sakandire.

Fitaccen mawaki kuma dan wasan kwaikwayo a masana'antar, Adam A. Zango ya biya wa wasu marayun yara kudin makarantar shekaru uku na sakandire a Zaria, jihar Kaduna.

Hukumar makarantar ta bayyana hakan kuma jarumin ya bai wa jaridar Premium Times kwafin rasit din.

A ranar 16 ga watan Nuwamba ne jarumin ya kai ziyara fadar Sarkin Zazzau. Sarkin ya mika godiyarsa ga jarumin saboda damar tallafin karatu da ya kawo masarautar.

2. Rahama Sadau da Fati Washa sun karba lambar yabo a Landan.

Jarumai Rahama Sadau da Fati Washa sun karba lambar yabo a bikin fina-finan Afirka kashi na 23 da aka yi a birnin Landan.

Anyi taron ne a tsohon dakin taro dake Broadway, Stratford, Landan a ranar 2 ga watan Nuwamba 2019.

DUBA WANNAN: Shehu Sani: An kara kama wani babban dan kasuwa a Kaduna

3. An nada Fati Nijar a matsayin sarauniyar mawakan hausa ta Turai.

A wani biki da aka yi a Paris, Sarkin Hausawan Turai, Sirajo Jan Kado ya nada mawakiya Fati Nijar a matsayin sarauniyar mawakan hausa ta Turai

An yi wannan shagalin bikin ne a fadar sarkin hausawan dake birnin Paris a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2019.

4. An karrama Ali Nuhu a Indiya.

Jarumi kuma Furodusa a masana'antar, Ali Nuhu ya samu lambar yabo daga daliban arewacin Najeriya dake karatu a Indiya.

Kungiyar daliban ce ta gayyaci jarumi Ali Nuhu don ya taya su murnar zagaoyawar ranar Hausa a can kasar Indiya din.

5. Maryam ta sanar da kwangila biyu da ta samu a 2019.

Jaruma Maryam Booth ta samu kwangilar talla da kamfanin Airtel da na Ajinomoto a shekarar 2019, kamar yadda ta bayyana.

Jarumar ta zanta da jaridar Premium Times a yayin da take sanya hannu a kan kwangilar tallar a garin Legas. Tun a watan Janairu ne ta samu na kamfanin Airtel, inda ta samu na Ajinomoto a watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel