Za mu cigaba da aiki tare don ciyar da Arewa gaba – Gwamnonin Arewa ga Buhari

Za mu cigaba da aiki tare don ciyar da Arewa gaba – Gwamnonin Arewa ga Buhari

Kungiyar gwamnonin yankin Arewacin Najeriya 19 sun dauki alkawarin cigaba da aiki kafada da kafada da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kawo cigaba mai daurewa ga jama’an Arewa da ma yankin gaba daya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jahar Filato ne ya bayyana haka cikin sakon murnar shiga sabuwar shekara daya fitar a ranar Laraba, 1 ga watan Janairun 2020.

KU KARANTA: Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Mista Lalong yace za su yi aiki da shugaba Buhari don samar da manyan ayyukan cigaba a Arewa, inda yace a haka ne za’a iya samar da hadaddiyar kasa, kuma dunkulalliya da ta samu cigaba da kuma adalci.

“Akwai alamun nasara a shekarar 2020 ga Najeriya, musamman ta bangaren tsare tsaren inganta tattalin arziki, da kuma karfafa gwamnatoci a mataki daban daban, don haka akwai bukatar buri mai karfi, aiki tukuru da kuma sadaukar da kai domin gina kasa mai karfi da ta dogara da kanta.

“Kungiyar gwamnonin Arewa za su cigaba da aiwatar da tsare tsare masu inganci a bangarorin da suka hada da kawar da talauci, yaki da jahilci, kawar dsa cututtuka da kuma tsaro da suka addabi yankin.” Inji shi.

Daga karshe Gwamna Lalong ya tabbatar da cewa matsalar tsaro ta kawo babbar koma baya ga cigaban yankin Arewa, amma yace hadin kan jama’an gari zai taimaka matuka wajen kawo karshen masifar, tare da karya duk wani dake burin tayar da hankalin jama’a.

A wani labarin kuma, babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai ziyara ga dakarun rundunar Sojin Najeriya dake bakin daga suna fafatawa da yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Buratai ya karasa zuwa kwalejin horas da Yansanda dake Limankara a garin Gwoza inda ya hau har can saman tsaunin Gwoza a ziyarar rangadin daya kai yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel