Uwa da 'Ya sun sheka barzahu bayan fasto ya basu jikon magani sun sha

Uwa da 'Ya sun sheka barzahu bayan fasto ya basu jikon magani sun sha

- Wata mata 'yar asalin kasar Zimbabwe da mahaifiyarta sun rasa ransu bayan da suka sha gubar da fasto ya basu

- Sun garzaya wajen faston ne da koken cewa Sithandazile bata samu miji ba har a lokacin da ta kai shekaru 30

- Ya basu wasu kwayoyi da suka sa su amai a take kuma ya basu wani ruwan da suka sha washegari wanda yayi sanadin mutuwarsu

Wata mata 'yar asalin kasar Zimbabwe da mahaifiyarta sun rasa ransu bayan da suka sha wani tsumi da fasto ya basu.

Sithandazile Nyathi mai shekaru 30 a duniya tare da mahaifiyarta Thokozani Ncube mai shekaru 51 sun rasu ne bayan da suka sha wani ruwan 'tsarkakewa' da wani fasto mai suna Brian Mpofu ya basu a cikin kwanakin karshen mako.

Rahoton ya bayyana cewa, matan biyu sun ziyarci faston ne don shawo kan matsalolin Sithandazile wadanda suka hada da rashin tsayayyen saurayi balle miji.

Seyiso Ncube tana mu'amala da faston tun tana kasar Afirka ta Kudu.

A yayin da Elizabeth Ncube ke zantawa da manema labarai, ta ce: "Ba ma nan a lokacin da abin ya faru. An sanar mana cewa sun je wajen wani fasto a Cowdray Park a ranar Asabar. Sithandazile ce ke bukatar taimakon faston kuma ta tafi tare da mahaifiyarta. Sun je ne tare da wata 'yar yayarmu mai shekaru 15 wacce ta bamu labarin abinda ya faru."

KU KARANTA: Yarinya 'yar shekara 13 ta mutu a lokacin da take haifewa mahaifinta cikin shegen da ya dirka mata

Tace, faston ya basu wani abu guda uku da suka sa su amai. Faston yace wannan aman ne ya fitar da sihirin da aka yi musu. Bayan nan ne ya basu wani tsumi wanda yace su sha washegari da safe kafin su ci komai.

Bayan shan wannan tsumin ne faston ya turo musu sakon waya cewa su biyu kacal zasu sha. Bayan shan wannan maganin ne suka ce cikinsu na ciwo.

Daga nan sai suka fara tunanin ko haka maganin yake aiki don haka basu fara tunanin kakalo amai ba. Bayan kawunmu ya shigo ne ya tarar da farar kumfa a bakinsu kuma sun fadi kasa a mace.

Babban sifetan 'yan sandan yankin, Precious Simango ya yi magana a kan lamarin. Ya ce: "Mun samu rahoton yadda wani fasto ya ba uwa da 'ya guba suka sha suka mutu. Ba zan iya magana mai yawa ba saboda hakan zai iya bata mana bincike. Mun damke wanda ake zargin amma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel