Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai ziyara ga dakarun rundunar Sojin Najeriya dake bakin daga suna fafatawa da yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Buratai ya karasa zuwa kwalejin horas da Yansanda dake Limankara a garin Gwoza inda ya hau har can saman tsaunin Gwoza a ziyarar rangadin daya kai yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

KU KARANTA: Abdulmuminu Jibrin ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai ma shugaban kasa Buhari

Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga
Source: Facebook

Wannan kwaleji na daga cikin cibiyoyin jami’an tsaro da Boko Haram ta taba kamawa a lokacin da take ganiyar cin karenta babu babbaka a shekarar 2014, a wancan lokaci, gaba daya karamar hukumar Gwoza ta kasance a hannun Boko Haram, har zuwa shekarar 2015 da Sojoji suka kwace ta.

Buratai ya zagaya cikin kwalejin don ganin matakin da aikin sake gina kwalejin ya kai, sa’annan ya yi karo da jama’an garin Gwoza da suka yi ta kai masa gaisuwa tare da bayyana godiyarsu a gare shi bisa namijin kokarin da yake yi don tabbatar da tsaro a yankin.

Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga
Source: Facebook

A cewar Buratai: “Idan baka san halin da mutum yake ciki ba ba zaka fahimce shi ba, na hau saman tsaunukan nan ne domin na ji yadda Sojoji suke ji a kullum idan sun hau saman nan, tare da doguwar tafiya a kasa.

“Haka zalika hakan zai kara musu kwarin gwiwa saboda na hau sama ba tare da sun yi tsammani ba, ganina da suka yi zai musu kaimi, kuma mun jaddada musu cewa muna sane dasu.” Inji shi.

Daga karshe Buratai ya taya Sojojin da ma jama’an garin Gwoza murnar shiga sabuwar shekara, inda ya kara da kira a garesu dasu cigaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya ta hanyar basu bayanan sirri da zasu taimaka wajen kawo karshen yakin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel