Yanzu Yanzu: Bala Mohammed ya amince da biyan ma’aikata karancin albashi N30,000

Yanzu Yanzu: Bala Mohammed ya amince da biyan ma’aikata karancin albashi N30,000

- Gwamnatin Bala Mohammed na jihar Bauchi ta amince da biyan ma'aikata a jihar karancin albashi na N30,000

- Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga Mohammed Baba, sakataren gwamnatin jihar

- Sabon umurnin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, daga ranar 1 ga watan Janairu, 2020

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da biyan ma'aikata a jihar karancin albashi na N30,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga Mohammed Baba, sakataren gwamnatin jihar zuwa ga manema labarai a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, a Bauchi.

A cewar jawabin, sabon umurnin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, daga ranar 1 ga watan Janairu, 2020.

"Mai girma Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohamme, ya karbi rahoton kwamitin hukumar ma'aikata na jihar kan aiwatar da sabon karancin albashi na kasa wanda ya ke N30,000 kamar yada gwamnatin tarayya ta tsara.

KU KARANTA KUMA: Manyan ayyuka 12 da gwamnatin Buhari za ta kammala a 2020 – Shugaban kasa ya tabbatar

"Don haka Gwamnati ta amince da biyan ma'aikatan jihar N30,000 a matsayin karancin albashi, fara daga ranar 1 ga watan Janairu, 2020," inji sakataren gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel