Fusatattun matasa sun kone motocin dakon siminti na kamfanin Dangote guda biyu

Fusatattun matasa sun kone motocin dakon siminti na kamfanin Dangote guda biyu

Wasu fusatattun matasa sun kone motocin dakon siminti na kamfanin Dangote bisa zargin cewa sun take mutane biyu har lahira.

Lamarin ya faru ne ranar Talata a garin Imowo dake yankin karamar hukumar Ijebu-Ode a jihar Ogun.

Matasan sun kone motocin ne sakamakon take wani dan acaba da fasinjan da ya dauko da motar dakon simintin ta yi yayin da suke wuce wa ta garin.

Kakakin hukumar tabbatar da biyayya ga dokokin tuki a jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Akinbiyi ya bayyana cewar mummunan hatsarin da ya afku a tsakanin motar kamfanin Dangote da dan acaban, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.

Fusatattun matasa sun kone motocin dakon siminti na kamfanin Dangote guda biyu
Motar kamfanin Dangote
Asali: UGC

"An samu wani mummunan hatsari a tsakanin motocin kamfanin Dangote guda biyu da dan acaba a garin Imowo dake yankin karamar hukumar Ijebu-Ode."

DUBA WANNAN: Cunkuson Apapa: Dangote ya yi asarar biliyan N25 a cikin shekara biyu

"Mutum biyu dake kan babur din da hatsarin ta ritsa da shi sun mutu nan take, lamarin da ya fusata matasan garin har suka cinna wa motocin kamfanin Dangote biyu wuta tare da hana a dauke gawar mutanen biyu da suka rufe a gefe guda," cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng