Yanzu-yanzu: FG ta nada Saratu Shafii a matsayin shugabar CAC

Yanzu-yanzu: FG ta nada Saratu Shafii a matsayin shugabar CAC

Gwamnatin tarayya ta nada Saratu Shafii a matsayin shugabar hukumar yi wa kamfanoni rijista (CAC). Hukumar ta sanar da hakan ne a takaitacciyar takardar da ta fitar a ranar Talata, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

"Muna farin cikin sanar da jama'a cewa an nada Hajiya Saratu Mama Shafii a matsayin mukaddashin shugabar hukumar yi wa kamfanoni rijista ta CAC. An sanar da nadin nata ne a wata wasika mai kwanan wata 30 ga watan Disamba 2019 ,wacce ta fito daga masana'aikatar masana'antu, siye da siyarwa da saka hanneyen jari." in ji takardar.

Har zuwa lokacin da aka nada ta, Shafii na daya daga cikin 'yan kwamitin yardaddu na hukumar. Nadin nata ya biyo bayan umarnin kotun laifuka na musamman na cewa Azuka Azinge ta sauka sakamakon karya da tayi wajen bayyana kadarorinta.

DUBA WANNAN: Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

An gurfanar da Azinge ne a gaban kotun laifuka na musamman a kan laifuka 11 da ake zarginta dasu a ranar 23 ga watan Disamba. An zargeta da karbar wasu alawus da ba hakkinta ba. A don haka cibiyar ta yanke cewa bai kamata ta cigaba da shugabantar CAC ba.

A hukuuncin kotun laifuka na musamman, ta amince da cewa Azinge ya sauka daga shugabancin hukumar har zuwa lokacin da kotun ta kammala sauraron karar tare da yanke mata hukunci.

Daga nan ne kotun sauraron laifuka na musamman din ta dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Janairu 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel