Tsohon IGP Idris ya karyata ikirarin shiga siyasar Neja

Tsohon IGP Idris ya karyata ikirarin shiga siyasar Neja

Tsohon sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris Kpotu, ya nesanta kansa daga wani kamfen din siyasa na bogi da ke yawo a yanzu a kafafen sadarwa, karkashin taken, shirin ceto.

A wani jawabi daga kakinsa, Bala Ibrahim, ya ce: “An janyo hankalin Tsohon Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim K. Idris zuwa ya wani kamfen din siyasa na bogi

“Ba wai kawai Idris na nesanta kansa daga hakan bane kawai, harma da gargadin wadanda suka dauki nauyin lamarin da su janye daga hakan daga yanzu, ko kuma su fuskanci hukunci.

"Abu na musamman da ya fi sanya damuwa shine taken kudirin ceto, wanda hakan ya sa abun ya nuna kamar akwai rikici tsakaninshi da gwamnatin jihar Niger mai mulki.

"Tabbass wadanda suka dauki nauyin lamarin sun tuntube shi a baya, kan kudirinsu na tsayar dashi takarar gwamna, inda ya fada masu cewa a’a, bai da ra’ayin siyasa a yanzu.

“Dalilin da ya sanya su cigaba kamfen dinsu mai cike da mugunta, ya kasance abun damuwa da sanya kokwanto.

KU KARANTA KUMA: Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke hanyar titin Lagas-Ibadan

“Yayinda ake shawartan jama’a da su yi watsi da kamfen din, ana gargadin wadanda suka dauki nauyin lamarin da su kwana da sanin makomar hakan, wanda baya da kasancewarsa zamba, ya kuma kasance kokarin kawo fita a tsarin da kuma haddasa rashin aminci a jihar."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel