An binne yaro matashi da ransa a cikin wani kango a Kano - Kwamishinan 'yan sanda

An binne yaro matashi da ransa a cikin wani kango a Kano - Kwamishinan 'yan sanda

Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano sun gano gawar wani yaro matashi, da aka boye sunansa, da ake zargin wasu mutane da binne shi da ransa a cikin wani kango dake kauyen Wase a yankin karamar hukumar Minjibir.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa ta kama mutane biyu; Aminu Suleiman, mai shekaru 29, da Abdulrashid Isha, mai shekaru 32, mazauna unguwar Tudun Murtala, bisa zarginsu da hannu a kisan matashin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Habu Sani, ne ya sanar da faruwar hakan a cikin wani jawabi da ya raba wa manema labarai ta hannun kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna.

Kwamishina ya bayyana cewa Suleiman da Ishaq sun sace yaron mai shekaru 11 a unguwar Kwana Hudu a cikin watan Nuwamba, inda suka bashi kayen maye sannan suka tafo da shi zuwa kangon da suka binne shi da ransa.

Ya kara da cewa masu laifin sun gudu sun buya a jihar Kaduna, inda aka kamo su, bayan ta'addanci suka aikata a watan Nuwamba.

An binne yaro matashi da ransa a cikin wani kango a Kano - Kwamishinan 'yan sanda

Wasu masu satar kananan yara tare da safararsu zuwa kudu da rundunar 'yan sanda ta yi holinsu a Kano
Source: Facebook

A cewarsa, "mun bi sahun wasu masu garkuwa da mutane; Aminu Suleiman mai shekaru 29 da Abdulrashid Ishaq mai shekaru 32, har jihar Kaduna inda muka kamo su bisa zarginsu da sace wani yaro mai shekaru 11 tare da binne shi a raye bayan sun bashi kayen maye da suka gusar masa da hankali.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar hana cakuda Maza da Maza a adaidaita

"Mutanen, mazauna unguwar Tudun Murtala, sun binne yaron a wani kango dake kauyen Wase a yankin karamar hukumar Minjibir, bayan sun sace shi a unguwar Kwana Hudu dake yankin karamar hukumar Ungoggo a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2019."

Kazalika, kwamishinan ya kara da cewa rundunar 'yan sandan jihar ta kama dumbin wasu laifi da suka hada da masu garkuwa da mutane da kuma wani kasurgumin dan ta'adda, Aliyu Mohammed, da aka sani da 'Ali Kwara'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel