PDP ta kalubalanci Buhari ya wallafa abin da fadar shugaban kasa ta ke batarwa

PDP ta kalubalanci Buhari ya wallafa abin da fadar shugaban kasa ta ke batarwa

Mun ji cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama abin koyi ta hanyar wallafa duk kashe-kashen fadarsa.

Jam’iyyar hamayyar ta na son shugaban kasar ya yi wannan ne domin hukumomin gwamnatin tarayya da ma’aikatu su ji dadin koyi da umarnin da ya bada.

Kamar yadda mu ka samu labari, PDP ta yi wannan jawabi ne a jiya Ranar 30 ga Watan Disamba, 2019, ta bakin Sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan.

Mista Kola Ologbondiyan ya na ganin cewa umarnin da shugaba Buhari ya ba dukkanin MDAs ba zai wadatar ba, har sai ya yi aiki a kan fadar shugaban kasa.

PDP ta ce akwai bukatar fadar shugaban kasar da ake warewa biliyoyi daga cikin kasafin kudi ta bayyana duk abin da ta ke kashewa, da yadda ake raba kwangiloli.

KU KARANTA: An fara rade-radin inda 'Dan takarar PDP zai fito a zaben 2023

Ba a nan kadai jam’iyyar adawar ta tsaya ba, ta bukaci a fito da jerin sunayen duk wadanda ake ba kwangila, da adadin kudin da aka kashe da kuma aikin da aka yi.

Ologbondiyan ya ke cewa ‘Yan Najeriya sun cancanci ayi masu ke-ke-da-ke na inda kudinsu su ke, don haka ya nemi a rika fadin yadda ake biyan kudin kwangila.

“Watakila wannan zai bayyana abin da ya sa wasu na kusa da fadar shugaban kasa su ke facaka da dukiya, su na rayuwa mai tsada a kasar da miliyoyi su ke wahala.”

“Abin takaici ne gwamnatin Buhari ba ta iya fito da kasafin kudinta a fili, duk da yawan kiran da ta ke yi na gaskiya, wanda ya ke nuna akwai abin da ake boyewa.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel