Rundunar sojin Najeriya za ta janye dakarunta daga arewa maso gabas

Rundunar sojin Najeriya za ta janye dakarunta daga arewa maso gabas

Rahotanni sun kawo cewa rundunar sojin Najeriya za ta fara janye jami’anta daga yankin arewa maso gabas daga shekarar da za a shiga.

Babban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe-Ibas ne ya bayyana hakan bayan ganawarsu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Ekwe-Ibas ya jadadda cewa za a janye sojin ne daga wasu yankunan kasar nan da rubu’in sabuwar shekara don mayar da hankalinsu kan wasu sabbin kalubale da ke danno kai, yayinda yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da civil defence Za su maye gurbinsu.

Ya Kara da cewa akwai bukatar yin haka don tabbatar da kwazon yan sandan kasar da jami’an civil defence wajen jan ragamar kula da yankunan arewa maso gabas.

Har ila yau, ya bayyana cewa alhakin kula da tsaron cikin gida ya ta’allaka ne a wuyan rundunar yan sanda, inda ya kara da cewa sojoji na kawo agaji ne da zaran lamura sun tabarbare wa yan sanda, sannan cewa muddin lamuran suka daidaita, babu abunda ya ragewa sojin face ficewa don mikawa yan sanda ragamar ci gaba da kula da tsaro.

Ya tunatar da al’umar kasar shirin gwamnatin shugaba Buhari na daukar sabbin jami’an ‘yan sanda dubu 10 domin cike gurabe, yana mai fatan sabbin daukar za su samu cikakken horo.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun kashe mutum 1, sun sace uwa da danta

A cewar babban hafsan, ba za su iya ci gaba da dankwafar da sojojin kasar wuri guda ba musamman ganin cewa, an cimma burin da ake fata a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Sai dai wasu bayanai na cewa, sai an tantance sha’anin tsaro kafin daukar matakin a arewa maso gabashin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel