2019: Daure Kalu, sakin Dasuki da sauran abubuwan da su ka faru a kotu
Mun tsakuro jerin wasu hukunci da kotu su ka yi a Najeriya a cikin wannan shekarar da ake bankwana da ita, wanda su ka bada mamaki. Daily Trust ta fara kawo wannan rahoto.
1. Sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore
Bayan shekaru fiye da hudu a garkame, gwamnatin tarayya ta saki Kanal Sambo Dasuki wanda Alkalai da-dama sun dade da bada belinsa. Haka zalika an saki Omoyele Sowore daga kaso.
2. Tsige Alkalin Alkalai
A farkon shekarar nan ne shugaban kasa ya dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onnoghen, daga aiki, ya kuma nada Tanko Mohammed, a kujerarsa, bayan an kai shi kotu.
3. An kama Fastoci da laifin fyade
Alkali ya samu Fasto Princewill, Adeleke da laifin yi wa ‘Yar shekara 14 fyade da zubar mata da ciki. Haka zalika an kama Johnson Adeleke da irin wannan laifi, wanda duk aka daure su.
4. IMN
Gwamnatin tarayya ta samu takarda daga kotu wanda ta jefa kungiyar IMN ta Mabiya addinin shi’a a cikin jeringiyar kungiyoyin ta’adda a Najeriya, bayan wata mummunar zanga-zanga.
KU KARANTA: Atiku ya na sa baki domin a saki ‘Dan Jaridar da aka kama
5. P&ID da Najeriya
Alkalan wani kotu da ke kasar Birtaniya sun yanke hukuncin cewa gwamnatin Najeriya za ta biya kamfanin P&ID kudi har Dala biliyan 9.8 saboda sabawa wata yarjejeniyar gas da ta yi.
6. Gurfanar da Abdulrasheed Maina
A cikin Watan Oktoba ne jami’an hukumar EFCC su ka gurfanar da Abdulrasheed Maina a gaban kuliya tare da ‘Dan sa mai suna Faisal. An tuhumesa da laifuffuka 12 bayan dogon dako.
7. Orji Uzor Kalu
A Disamban nan ne Alkali ya samu tsohon gwamna Orji Kalu da laifin wawurar Biliyan 7.56, wannan ya sa aka yankewa Sanatan na APC hukuncin daurin shekaru 12 tare da wani Yaronsa.
8. Masu cin albashi da fansho
Wani babban kotun tarayya da ke zama a Legas ya yanke hukuncin cewa duk tsohon gwamna da ya ke majalisa ko kuma ya ke rike da kujerar Minista, ya dawo da fanshon da ake biyansa.
9. Shari’ar zaben 2019
Alkalan kotun koli sun ba gwamnoni 8 da ka rike da kujeru gaskiya a shari’ar zaben 2019. Haka zalika babban kotun kasar ya yi fatali da karar Atiku Abubakar game da zaben shugaban kasa.
Kafin nan kotun sauraron karar zabe da na daukaka kara sun ba APC gaskiya a zaben jihar Kano.
10. Rijiyoyin man Soku
Kuliya ta tabbatar da cewa rijiyoyin man Soku na Ribas ne. A wannan shekarar Alkalai su ka raba gardama a shari’ar da ake yi tsakanin jihar Bayelsa da makwabciyar ta Ribas a Neja-Delta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng