Rikici guda 6 da suka wakana a Kannywood cikin shekarar 2019

Rikici guda 6 da suka wakana a Kannywood cikin shekarar 2019

Furodusoshi sun bayyana cewa ba a sayen fina-finai a wannan shekarar saboda haskasu da ake yi a sinima

Haka zalika anyi fadace-fadace tsakanin jarumai da dama a masana’antar Kannywood wanda hakan ya jawo tashin-tashina da yawa.

Ga wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru guda shida a masana’antar Kannywood a cikin wannan shekara ta 2019:

1. Ali Nuhu Ya Maka Adam Zango a Kotu

Anyi wannan fadan ne a watan Afrilu, inda Ali Nuhu ya maka Adam A Zango a kotu sakamakon zarginsa da yake da bata masa suna.

A wani bidiyo da Adam A Zango ya fitar, ya zargi Ali Nuhu da goyon bayan magoya bayansa don sun zagi mahaifiyarsa. Da farko dai Ali Nuhu bai mayar da martani ba, amma daga baya ya kaishi kotu. Sa hannun manyan masana’antar ne yasa ya janye wannan karar.

2. Zahraddeen da Zeezee Sunyi Fada Saboda Wani Kudi da Atiku ya Bada

Jaruman biyu sunyi kaca-kaca ne sakamakon zargin juna da suke yi a kan rub da ciki da wasu kudade da Atiku ya basu.

Zeezee ta zargi Zahraddeen da bata kaso kadan daga cikin kudin. Ta kuma zargi Sani Danja, Fati Mohammed, Al’amin Buhari da Imrana Mohammed da diban kudin da Atiku ya bawa masana’antar don amfanin kansu. Daga baya Zahraddeen ya kai kararta wajen ‘yan sanda amma ya janye bayan da aka sanya baki a maganar.

3. Hadiza Gabon da Amina Amal

A shekarar 2019 dinnan ne da muke bankwana Hadiza Gabon ta je har gida ta yiwa Amal dukan tsiya sakamakon zarginta da tayi da madigo. Bayan haka ta dau bidiyo ta saka a shafin Instagram, lamarin da ya jawo hankulan masu kare hakkin dan Adam.

Daga baya dai an sasanta su, amma har yau basa ga maciji a junansu.

4. An zargi Zango da diban yara kanana don yin sabbin fina-finai

Wani Malami ya zargi Adam Zango da diban kananan yara don fitowa a sabbin fina-finansa. Malamin ya zargi Zango da yin amfani da damar wajen sanya yaran su bar karatu don komawa wasan fim.

Bayan kwanaki kadan, Zango ya fito tare da rantsuwa da Qur’ani wajen karyata zargin Malamin, inda wannan lamari ya jawo kace-nace matuka.

5. Auren Mutu’a a Kannywood

A cikin wannan shekarar ne dai Sadiya Haruna ta zargi jarumi Isa A Isa da yin auren mutu’a da ita inda ta dinga yin bidiyo tana fadar maganganu na batanci a kansa gami da cewa tana da hujjojin ta, lamarin da ya kai ga Isa yasa aka kama Sadiya daga baya kuma aka sako ta, sai dai kuma bayan da aka zauna shari’ar an tura Sadiya zaman jiran shari’a na ‘yan kwanaki a gidan yari kafin daga baya aka bayar da belin ta.

6. An kalubalanci shigar Rahama Sadau a wajen bikin ranar haihuwarta

Da yawa daga cikin ‘yan fim sun fito sun kalubalanci jaruma Rahama Sadau akan shigarta a wajen taron bikin da tayi na zagayowar ranar haihuwarta.

Bayan haka jarumar ta kuma bude wajen cin abinci tare da gidan shan shisha, lamarin da ya jawo kace-nace daga wajen mutane da dama.

Kamar dai yadda tashar YouTube ta tsakar gida ta wallafa, akwai abubuwa da dama da suka faru a masana’antar, amma wadannan sune wadanda suka yi fice.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel