Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar hana cakuda Maza da Maza a adaidaita

Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar hana cakuda Maza da Maza a adaidaita

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da kaddamar da dokar haramta cakuda Maza da Mata tare a cikin baburan adaidata sahu da ake amfani da su wajen jigilar jama'a.

A cikin makon jiya ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar, ta bakin babban kwamandan hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, cewa dokar haramta cakuda Maza da Matan zata fara aiki ne daga watan Janairu na sabuwar sheakarar 2020.

Jaridar Solacebase dake Kano ta rawaito cewa majiya mai karfi daga cikin gwamnati ta sanar da ita, a daren ranar Litinin, cewa gwamna Ganduje ya dakatar da kaddamar da dokar ne saboda rudanin da ta fara kawowa tun yanzu tare da tabbatar da ganin cewa kaddamar dokar bai haifar da rikici ba.

Tun a makon jiyan Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta haramtawa mutane mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya a fadin jihar daga watan Janairu 2020.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin rufe bikin IVC da aka yi karo na 77 wanda kungiyar musulmai ta kasa ta shirya. Hakan ya faru ne jami'ar Bayero dake Kano.

Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar hana cakuda Maza da Maza a adaidaita

Ganduje
Source: Twitter

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya ce gwamnatin jihar ta shirya tsaf wajen jaddada hukunce-hukunce addinin Islama.

Kamar yadda aka sani, an fara gabatar da adaidaita sahu ne a jihar Kano tun zamanin mulki Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin sufuri ga mata zalla.

DUBA WANNAN: An binne yaro matashi da ransa a cikin wani kango a Kano - Kwamishinan 'yan sanda

Wannan ya biyo bayan haramta achaba daga daukar mata da tsohon gwamnan yayi.

Tun bayan saukar Malam Shekarau, adaidaita sahu sun koma daukar kowanne jinsi, lamarin da gwamnatin yanzu ta ce ba zata lamunta ba.

Hakazalika, Gwamna Ganduje ya yi kira ga daliban da su fuskanci karatunsu tare da watsi da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel