Cunkuson Apapa: Dangote ya yi asarar biliyan N25 a cikin shekara biyu

Cunkuson Apapa: Dangote ya yi asarar biliyan N25 a cikin shekara biyu

- Gwamnatin tarayya ta fara gyaran hanyar zuwa tashar ruwa dake yankin Apapa a jihar Legas domin magance cunkuson ababen hawa

- Shugaban rukunin masana'antun Dangote, Aliko Dangote, ya ce wasu kamfanoninsa guda biyu sun yi asarar fiye da biliyan N25 a cikin shekara biyu

- Dangote ya bayyana hakan ne a gaban ministan aiyu da gidaje, Babatunde Fashola, yayin ziyarar ganin aikin da ya kai a ranar Asabar

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfanoninsa guda biyu dake yankin Apapa sun yi asarar fiye da biliyan N25 a cikin shekaru biyu sakamakon cunkuson ababen hawa da ake samu a yankin.

Dangote ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake tare da ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, a wurin duba aikin hanyar Apapa da ake yi.

Cunkuson Apapa: Dangote ya yi asarar biliyan N25 a cikin shekara biyu
Aliko Dangote
Asali: UGC

"Muna aiki ne a yankin da tashar ruwa ta Apapa take. Idan aka duba kudin shigar da kamfanoninmu biyu suka samu daga shekarar 2017 zuwa 2018, mun yi asarar fiye da biliyan N25 saboda cunkuson ababen hawa.

DUBA WANNAN:

"Muna sarrafa kayan, babu wata matsala dangane da hakan, amma babbar matsala ita ce yadda zamu fitar da kayanmu daga masana'antun zuwa kasuwa ko wurin ajiyar manyan dilolinmu," Dangote ya bayyana cikin takaici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel