Disamba: Sabon tsarin karin albashin da gwamnatin Kano ta yi wa ma'aikatanta a matakai daban - daban

Disamba: Sabon tsarin karin albashin da gwamnatin Kano ta yi wa ma'aikatanta a matakai daban - daban

Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ma'aikatanta sabon tsarin karin mafi karancin albashin N30,000 a karshen watan Disamba.

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun amince a kan yin karin kaso 23.2% ga ma'aikatan dake mataki na 7, kaso 20% ga ma'aikatan dake mataki na 8 da kuma yin karin kaso 19% ga ma'aikatan dake mataki na 9.

Tun a ranar 18 ga watan Afrilu, 2019, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar yin karin albashi.

Sai dai, bayan kungiyar NLC ta kammala cimma matsaya da gwamnatin tarayya, rigimar biyan sabon karin mafi karancin albashin ta koma jihohi.

Bayan jerin ganawa a tsakaninsu a kan sabon karin albashin, gwamnonin jihohi sun amince a kan cewa kowacce jiha ta je ta kara adadin da zata iya biya.

Disamba: Sabon tsarin karin albashin da gwamnatin Kano ta yi wa ma'aikatanta a matakai daban - daban

Gwamnan jihar Kano; Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa a kan karin albashi ya kammala aikinsa tare da cimma matsaya yayin zamansa na ranar 19 ga wata a kan fara biyan sabon karin albashin daga karshen watan Disamba na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: APC: Manyan 'yan siyasa 5 da zasu iya taimakon Tinubu ya cimma burinsa a 2023

Bisa sabon tsarin biyan karin albashin, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta wallafa, gwamnatin Kano ta amince tare da fara biyan ma'aikatanta karin albashi kamar haka; karin kaso 14% ga ma'aikatan dake kan mataki na 09, karin kaso 11% ga ma'aikatan dake kan mataki na 10, karin kaso 10% ga ma'aikatan dake kan mataki na 12, da karin kaso 9% ga ma'aikatan dake kan mataki na 13.

Sai kuma karin kaso 8% ga ma'aikatan dake kan mataki na 14 da kuma karin kaso 6% ga ma'aikatan dake kan mataki na 15 zuwa 17.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel