Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Zamani ya kawo mu wani lokaci da galibin masoya masu niyyan aure su kan dauki hotunan kayatattu su wallafa a shafukan sada zumunta ko kuma su aika wa 'yan uwa da abokan arziki ana daf da daurin aure. Irin wadannan hotunan ne ake yi wa lakabi da hotunan kafin aure ko 'Pre-wedding Pictures'

A halin yanzu akwai wani hotunan kafin auren da na wani saurayi da budurwa inda budurwar ta murtuke fuska a dukkan hotunan wanda hakan ne nuna akwai alamar akwai wata matsala.

Domin mafi yawancin mata suna murna tare da daukin zuwan irin wannan ranar a rayuwarsu hakan yasa za ka ga sun caba ado da gyaran jiki kuma suna murmushi ko dariya a hotunan tare da masoyansu da ake fatan mutu ka raba.

Sai dai ita wannan budurwar da alamu ke nuna 'yar arewa ce ta fita daban domin ko kadan babu alamar annashuwa, farin ciki ko murna a tare da ita. Amma shi kuma saurayin nata ba bu alamar yana cikin wata damuwa.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

Wannan yanayin da budurwar ta fito a hoton ya ja hankulan al'umma masu amfani da shafukan sada zumunta inda suka rika tofa albarkacin bakinsu. Mafi yawancinsu na tambaya ko dai auren dole ne za a yi wa budurwa.

Ga dai hotunan a kasa:

Ga wasu kadan daga cikin abubuwan da mutane suka fadi kan hoton:

_sholie: "Ayyah, haka wannan yarinyar za ta jure wannan abin har abada"

el_sadeeq88: "Wannan yarinyar fa ba ta son yaron nan."

bature_d_3rd: "Kamar fa an tilasta mata auren shi ne"

firdausi5164: "Ana tilas ne, a kyale ta mana."

nabu_fashion_house: "Watakila hada su aka yi kawai"

homemade_delights_kn: "Yarinyar nan fa ba ta farin ciki ko kadan."

_amahh: "Wata kila haka fuskanta ya ke."

aliyah_kabs: "A'a, daga gani tana cikin damuwa."

hindatu_yabo: "Daga gani wannan tilasta aka yi. Allah ya taimake ta."

saddiq_jb: "Chap irin wannan ne ke kashe miji."

lolademartins: "Kaico yarinya, iyaye ba su zaba mata abinda ta ke so ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel