Wata sabuwa: An kirkiro sabuwar manhajar waya ta yiwa mata kishiya

Wata sabuwa: An kirkiro sabuwar manhajar waya ta yiwa mata kishiya

- A kasar Indonesia ne wani bawan Allah mai son tabbatar da sunna ya kirkiro wata manhaja ga maza masu son auren mace fiye da daya

- A wannan manhajar ce maza zasu iya samun mace don aure na biyu, uku ko hudu

- Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce daga mata masu fafutukar daidaituwar jinsi a kasar

A kasar Indonesia ne aka kaddamar da wata manhaja ga maza ma'aurata masu bukatar karin aure.

Ayopoligami sunan manhajar kuma ta jawo takaddama a kasar wacce tafi kowacce kasa yawan musulmai a fadin duniya. Wannan manhajar ta ba maza masu sha'awar karin aure damar yin hakan ba tare da sha'awar neman matan banza ba. A wannan manhajar, mazan zasu iya zantawa da maza 'yan uwansu masu irin wannan ra'ayi.

Lindu Pranayama ne mutumin da ya kirkiro manhajar da tunanin fasahar zata biya dumbin bukatun da ke akwai.

"Muna ganin wani al'amari inda maza masu yawan gaske ke neman kara aure amma idan suka je shafukan hada soyayya, ba sa ganin zabin yi wa matansu kishiya."

Ya ce, anyi musu tanadi don neman karin aure na biyu ko na uku ko na hudu.

Sai dai wannan ya jawo cece-kuce daga masu fafutukar daidaituwar jinsi a kasar. Sun dubi wannan manhaja a matsayin wacce take tunzura auren mace fiye da daya da kuma muzgunawa mata.

KU KARANTA: Gargadi: An gano yadda wuraren sayar da abinci ke sanya Paracetamol a cikin nama domin ya dahu da wuri

Wata mata mai rajin tabbatar da daidaituwar jinsi, Zakia Tunisa ta ce abin takaici ne da firgitarwa karon farko da ta ji batun wannan mahajar.

A cewarta, kafin ma a samar da manhajar kara aure, dama can auren mace fiye da daya ya yawaita.

Ta bayyana cewa manhajar na ingiza auren mata da yawa ya yawaita kuma a tilasta wa mata su yarda da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel