Za’a dauki mutane miliyan 1 aiki domin shuka bishiya guda dubu 300 a jahar Kaduna

Za’a dauki mutane miliyan 1 aiki domin shuka bishiya guda dubu 300 a jahar Kaduna

Wata kungiya mai zaman kanta, gidauniyar Aid Foundation ta bayyana cewa ta kammala shirin daukan ma’aikata miliyan daya domin su gudanar da aikin shuka bishiyu guda 300,000 a unguwanni 35 a fadin jahar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban daraktan kungiyar, Emmanuel Bonet ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba a garin Kaduna, inda yace zasu gudanar da aikin ne a shekarar 2020 a karkashin wani aiki na musamman mai taken “Koriyar zaman lafiya”.

KU KARANTA: Malam El-Rufai ne kadai ke da hurumin sakin Sheikh Zakzaky – gwamnatin tarayya

A cewarsa, manufar aikin shuka bishiyoyin ya kunshi habbaka zaman lafiya, rage radadin dumamar yanayi, kara wayar da kai a kan tsaftace muhalli, da kuma hankaltar da jama’a game da illolini ba haya a bainar jama’a.

Ya kara da cewa kawunan jama’an jahar Kaduna a rarrabe yake ta bangaren bambamce bambamcen addinai, don haka yake sa ran wannan aiki zai karfafa alaka tsakanin bangarorin biyu domin saman da hadin kai da zaman lafiya.

“Za mu dauki Musulmai da dama domin su aiwatar da shuka bishiyoyi a unguwannin kiristoci, haka zalika su ma matasan kirista za su shuka bishiyoyi a unguwannin Musulmai, matasan zasu share unguwannin, su amshi lambar wayoyin juna domin neman taimakon abokansu wajen shayar da shukokin ruwa.

“Idan na shuka bishiya a gaban gidanka, zan rokeka ka taimaka wajen bata ruwa, zan dinga kiranka lokaci zuwa lokaci don sanin halin da bishiyar take ciki, kuma zamu hadu akalla sau daya a wata daya mu yi hoto.

"Kuma mu duba halin da bishiyar take ciki. Idan aka cigaba a haka, hakan zai kara dankon zumunci a tsakanin matasa da kuma jama’an unguwannin.” Inji shi. Haka zalika shugaban kungiyar yace zasu gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar hukumar kula da kayayyakin gwamnati, KADFAMA.

Shima shugaban kungiyar matasan Najeriya reshen karamar hukumar Kaduna ta kudu, Zailani Musa, ya bayyana farin cikinsa da wannan aiki, kuma ya tabbatar da cewa zai kawo zaman lafiya a jahar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel