Ku nemi shawara kan aure daga mutanen kirki – Buhari ga matasan Najeriya

Ku nemi shawara kan aure daga mutanen kirki – Buhari ga matasan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba a Kano ya bukaci sabbin ma’aurata da su nemi shawara daga mutanen da za su fayyace mutu gakiya daga bangarori biyu kuma mutanen kirki, yayinda yake taya Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan murnar auren dansa.

Ibrahim, dan Shugaban majalisar dattawa, ya auri Ammani a Kano.

A wani sako, shugaba Buhari ya shawarci sabbin ma’auratan da su yi koyi da rayuwar Shugaban majalisar dattawan wanda ya bayyana a matsayin daidaitacce.

“Idan kuna neman wasu shawarwari kan rayuwa, wanda ya shafi kowani bangare, ya zama dole ku mayar da hankali sannan ku koya aga mutanen da ke da shaida mai kyau.

“Mutum nagari abun koyi shine Sanata Lawan. A siyasa da rayuwa, ya tara kyawawan dabi’u,” Shugaban kasar ya bayyana a wani sako da wata tawaga wacce ta hada da ministan Abuja, Mohammed Musa Bello, na tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (rtd), na noma, Sabo Nanono da kuma na sufurin jirgin sama, Hadi Sirika suka gabatar.

Sauran tawagar sun hada da babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin gida da taruka, Sarki Abba, kakain Shugaban kasa, Garba Shehu a kuma Ambasada Lawal Kazaure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel