Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama a Kazakhstan

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama a Kazakhstan

- A kalla mutane 15 ne suka mutu inda sama da fasinjoji 12 ke kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin jirgin sama

- Hatsarin ya faru ne a Kazakhstan yayin da jirgin saman ya tashi da mutane 100 a ciki inda ya doshi babban birnin jihar

- Shugaban kasa Tokayev-Jomart ya tabbatar da cewa zai tallafa wajen biyan diyyar wadanda suka rasa rayukansu kuma za a bincika silar hatsarin

A kalla mutane 15 ne suka mutu inda sama da fasinjoji 12 suka raunata a ranar Juma'a bayan da jirgin sama dauke da mutane ya rikito jim kadan bayan tashin shi daga babban birnin Kazakhstan, kuma ya fada kan wani gida.

Jirgin ya fado ne bayan mintoci kalilan da ya tashi daga birnin inda ya doshi babban birnin kasar mai suna Nur-Sultan dauke da fasinjoji 95 da kuma kungiyar matuka 5 a ciki, kamar yadda hukumomi suka sanar.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama a Kazakhstan
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama a Kazakhstan
Asali: Facebook

Ya fada kan wani shingen kankare zuwa wani bene mai hawa biyu wanda ke arewa maso gabas da filin sauka da tashin jiragen.

A wani bidiyo da kwamitin gaggawa na kasar ya fitar, ya nuna yadda jirgin ya tarwatse bayan da ya rushe gidan kafin 'yan taimakon gaggawa su iso.

Masu taimakon gaggawar sun yi kokari wajen fito da ragowar mutanen ta tagar jirgin kafin a mika su asibiti.

Shugaban cibiyar lafiya ta Almaty, Tleukhan Abildayev ya ce mutane 14 ne suka mutu a take yayin da wata matashiya daya ta rasu bayan isarsu asibiti.

Mutane 66 ne suka samu rauni, 50 daga ciki an kwantar dasu a asibiti inda 12 daga ciki ke cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA: Ba wai rawa da waka ne ke da muhimmanci a fim ba - Zulaihat ZPreety

A cikin wadanda suka samu raunin akwai yara kanana tara.

Babu kowa a cikin gidan da jirgin ya fada, kamar yadda gidan talabijin din Khabar ya ruwaito.

Shugaban kasa Kassym-Jomart Tokayev ya yi alkawarin samarwa iyalan wadanda abun ya ritsa dasu diyya kuma za a ladabtar da wadanda ke da hannu a wannan hatsarin.

Tokayev ya ce, gwamnati ta shirya kwamiti don bincikar yadda lamarin mai muni ya auku.

Ministan cikin gida ya ce, ma'aikatarsa ta kafa kwamitin bincike a kan yadda ake take dokokin sufurin jiragen saman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel