Mamaki: Yawan Musulmi ya zarce na Kiristoci a Cocina ranar Kirsimeti - Fasto a Kaduna (Hotuna)

Mamaki: Yawan Musulmi ya zarce na Kiristoci a Cocina ranar Kirsimeti - Fasto a Kaduna (Hotuna)

Yohanna Buru, wani Fasto dake zaune a Kaduna, ya ce Musulmin da suka halarci Cocin da yake jagoranta a ranar bikin Kirsimeti sun zarce adadin mabiya addinin Kirista.

A cewarsa, manyan malaman addinin Islama, masu rike da sarautar gargajiya da sauran kungiyoyin tabbatar da zaman lafiya daga jihohin arewa 19 sun halarci Cocinsa ranar bikin Kirsimeti.

Ya bayyana cewa hakan ya nuna cewa 'yan Najeriya zasu iya zama da juna lafiya duk da banbancin addini.

Da yake gabatar da huduba a Cocinsa dake unguwar Sabon Tasha a cikin garin Kaduna, Buru ya jaddada bukatar zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin mabiya mabanbantan addinai dake Najeriya.

DUBA WANNAN: Ganduje ya sake zama gwarzon gwamnonin APC

"Dole muke tuna cewa mun fito ne daga tsatso guda, saboda Annabi Adam ne ubanmu baki daya. Sannan muna da litattafai: Injila da Qur'an," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, "dukkanmu mun yarda da wuta da aljanna. A saboda haka, ya kamata mu kasance 'yan uwa masu kaunar junansu. Muna amfani da lokacin bikin Kirsimeti domin hada kan Muslmi da Kirista da kuma kara dankon zumunci a tsakaninsu."

Ya kara da cewa dukkan Musulmin duniya sun yarda annabi Isa tare da yin kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu jibintar lamarin 'yan uwansu domin samun zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban - daban.

Mamaki: Yawan Musulmi ya zarce na Kiristoci a Cocina ranar Kirsimeti - Fasto a Kaduna (Hotuna)
Musulmi sun halarci Coci ranar Kirsimeti a Kaduna
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel