Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano

Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano

- Wani matashi mai suna Abubakar Danjuma Maiwada ya kera keke mai iya tuka kanta a Kano

- Keken na amfani da kimiyyar hasken rana ne wajen tuki kuma ana iya cajin waya ko Laptop da ita

- Abubakar dai tsohon dalibin jami’ar BUK ne wanda ya karanaci fannin kimiyyar kere-kere ta kanikanci

Wani matashi mai hazaka daga jihar Kano mai suna Abubakar Maiwada Danjuma ya hada wata Keke wacce ke iya tuka kanta ta hanyar amfani da hasken rana.

Wannan matashin dai ya daura hotunan keken da ya samar ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda ya bayyana cewa keken za ta iya tuka kanta da kanta idan har matukinta ya gaji. Ya yi amfani da hanyar kimiyya da fasaha ne ya samar da ita. Tana kuma amfani ne da hasken rana.

Hakazalika, Abubakar ya kara da cewa, matukin Keken zai iya amfani da ita wajen cajin wayar salula da kuma na’urar tafi da gidanka, watau kwamfutar Laptop.

KU KARANTA: Hotuna: Daliban firamare a Katsina sun gaji da gafara sa, sun fara ginawa kansu ajujuwan karatu

Bincike ya bayyana cewa, Abubakar tsohon dalibin BUK ne kuma ya karanci fannin kimiyyar kere-kere ta kanikanci. Mahaifin Abubakar kuwa Farfesa Danjuma Maiwada, yana daya daga cikin manyan farfesoshin da jami’ar take ji da su.

Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano
Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano
Asali: Facebook

Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano
Hotuna: Hazikin matashi ya kera keke mai tuka kanshi da kanshi a jihar Kano
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng