Kasar Saudiyya ta haramta aure ga wadanda basu kai shekara 18 ba

Kasar Saudiyya ta haramta aure ga wadanda basu kai shekara 18 ba

- Ma'aikatar shari'a ta kasar Saudi Arabia ta haramta auren wadanda basu kai shekaru 18 ba

- Ministan shari'ar kasar, Sheikh Dr. Walid Al-Samaani ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin

- Kafin a kulla yarjejeniyar aure, dole ne mutanen su kasance sun wuce shekaru 18 kuma da amincewarsu

Ma'aikatar shari'a ta kasar Saudi Arabia ta haramta auren wadanda basu kai shekaru 18 ba a kasar. Ta kuma fitar da shekaru 18 su zama karancin shekarun da dan kasar zai iya aure.

Kamar yadda rahoto daga Saudi Gazette ya bayyana, ministan shari'a kuma shugaban majalisar koli ta shari'ar kasar, Sheikh Dr. Walid Al-Samaani, a ranar Litinin ya fitar da takardar ga dukkan kotun kasar.

Takardar ta jaddada haramcin auren yara masu karancin shekaru. Matukar wanda bai kai shekaru 18 ba ya yi aure a kasar, ya yi karantsaye ga doka kenan.

DUBA WANNAN: 'Yan bidiga sun zo kashe Jonathan ne - Dr. Tubo

Dukkan wata bukata an mika ta ga kwararrun kotun kasar don su kammala shirye-shiryen da suka yi dai-dai da dokar bada kariya ga kananan yara, tare kuma da tabbatar da kirkirarrun dokokin.

Umarnin Al-Samaani sun dogara ne da sakin layi na 16 a sashi na 3 na dokokin bada kariya ga kananan yara.

Dokar ta ce: "Kafin a kulla yarjejeniyar aure, dole ne a tabbatar da cewa wadanda za a aurar din sun kai 18 kuma hakan ba zai cutar da shi ko ita ba. Hakazalika kuma da yardarta ko shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel